Secondus, Atiku da Gwamnonin PDP sun gana kan shirye-shiryen Zaben 2019 a garin Abuja

Secondus, Atiku da Gwamnonin PDP sun gana kan shirye-shiryen Zaben 2019 a garin Abuja

A ranar Litinin din da ta gabata ne dan takarar shugaban kasa karkashin inuwa ta jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar tare da shugaban jam'iyya Uche Secondus da kuma zababbun gwamnoni na jam'iyyar, sun gana da juna a garin Abuja domin daura damarar babban zabe na 2019.

Ko shakka ba bu kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, karatowar babban zabe na 2019 ya sanya tsohon mataimakin shugaban kasa tare da gwamnoni da kuma shugaban jam'iyyar na kasa suka gana da juna domin shimfida tsare-tsare na tunkarar zaben cikin shiri.

Rahotanni sun bayyana cewa, abokin takarar Atiku, Peter Obi da kuma 'yan takara 29 na kujerun gwamnonin jihohin kasar nan, sun halarci wannan taro domin daura damararsu ta cimma nasara a zaben na badi.

Jaridar Legit.ng ta fahimci, ganawar jiga-jigan jam'iyyar ta fara gudana ne da misalin karfe 10.00 na daren ranar Litinin din da ta gabace mu zuwa wayewar gari na Talata.

Secondus, Atiku da Gwamnonin PDP sun gana kan shirye-shiryen Zaben 2019 a garin Abuja
Secondus, Atiku da Gwamnonin PDP sun gana kan shirye-shiryen Zaben 2019 a garin Abuja
Asali: Depositphotos

Secondus wanda ya jagoranci wannan taro ya shaidawa mambobin jam'iyyarsa musabbabin gudanarsa da ta kasance shimfida tsare-tsare da dabaru da jam'iyyar PDP za ta lallasa shugaban kasa Muhammadu Buhari da kuma jam'iyyarsa ta APC.

KARANTA KUMA: Farouk Lawan ya nemi cin hancin $500, 000 - Otedola ya shaidawa Kotu

Kazalika rahotanni sun bayyana cewa, ganawar jiga-jigan jam'iyyar ta yi tsokaci kan sakamakon zabukan maye gurbi da suka gudana a karshen makon da ya gabata cikin jihohin Katsina, Bauchi da kuma Kwara inda jam'iyyar APC ta lashe komai.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, akwai jihohin da zabukan kujerar gwamna ba za su gudana ba da suka hadar da; Ekiti, Osun, Ondo, Anambra, Bayelsa, Kogi da kuma Edo a yayin babban zabe na 2019.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel