Farouk Lawan ya nemi cin hancin $500, 000 - Otedola ya shaidawa Kotu

Farouk Lawan ya nemi cin hancin $500, 000 - Otedola ya shaidawa Kotu

Hamshakin dan kasuwar nan kuma fitaccen attajiri, Femi Otedolo, a yau Laraba ya fayyace yadda wani tsohon dan majalisar wakilai, Farouk Lawan, ya nemi cin hancin $500, 000 a wurinsa domin tsige sunan kamfaninsa daga cikin jerin wadanda ake zargi da zambar tallafin man fetur.

Kamar yadda shafin jaridar The Punch ya ruwaito, Otedola ya fayyace yadda tsohon dan majalisar wakilan ya nemi na goro a wurinsa domin tsige sunan kamfaninsa na Zenon Petroleum and Gas Limited daga cikin jeranton kamfoni da ake zargi da badakalar zamba ta tallafin man fetur.

Rahoton jaridar The Cable ya bayyana cewa, Otedole ya shaidawa babbar kotun tarayya da ke garin Abuja cewa, Lawan ya zame sunan kamfaninsa daga cikin jerin kamfonin man fetur da ake zargi da wannan laifi bayan ya karbe na goro a hannun sa.

Farouk Lawan ya nemi cin hancin $500, 000 - Otedola ya shaidawa Kotu
Farouk Lawan ya nemi cin hancin $500, 000 - Otedola ya shaidawa Kotu
Asali: Getty Images

Majiyoyin rahoto sun bayyana cewa, ana ci gaba da gudanar shari'a kan tsohon dan majalisar bisa zarginsa da karbar cin hanci domin zame sunan kamfanin fitaccen Attijirin daga cikin jerin kamfanoni da ake zargi da zambar tallafin man fetur.

Jaridar Legit.ng ta fahimci cewa, tsohon dan majalisar na jihar Kano na ci gaba da fuskantar dambarwar wannan zargi tun yayin da ofishin lauyan kolu ya fara tuhumarsa tun shekaru biyar da suka gabata.

KARANTA KUMA: Gwamna Bello zai bayar da Ladan N100m ga bayanai kan makasan Hadimin sa

Fitaccen dan siyasar ya kasance dan majalisa mai wakilcin kananan hukumomin Bagwai da Shanono a majalisar wakilai ta tarayya tun shekarar 2003 zuwa 2015.

Jaridar Legit.ng ta kuma ruwaito cewa, a watan da ya gabata ne Salihu Tanko Yakasai, kakakin gwamnan jihar Kano Abdullahi Umar Ganduje, ya yi ba'a ga Farouk Lawan dangane da wani faifan bidiyo da ya bayyanasa karara yayin da yake karbar cin hanci tun a shekarar 2012 da ta gabata.

Sanarwa: Ku ci gaba da kasancewa tare da mu yayin da Shafin Naij.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Domin shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

https://facebook.com/legitnghausa

https://twitter.com/legitnghausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel