DSS sun kama masu garkuwa da mutane da kuma likitan Boko Haram a wata jihar Arewa

DSS sun kama masu garkuwa da mutane da kuma likitan Boko Haram a wata jihar Arewa

Hukumar yan sandan farin kaya DSS, ta bayyana cew jami’anta da ke aiki tare da rundunar soji sun kama wani Yusuf Salisu wanda ake zargin likitan masu garkuwa da kuma yan Boko Haram ne.

An kama wanda ake zargin ne a ranar 9 ga watan Nuwamba, a kauyen Sabon Birbi, karamar hukumar Igabi, jihar Kaduna a cewar wata sanarwa daga kakakin DSS, Peter Afunanya.

Yace har zuwa lokacin da aka kama shi, ya kasance yana gudanar da wani dakin siyar da magani da kuma kula da masu garkuwa da mutane idan suka ji rauni.

DSS ta kuma ce Salisu na da nasaba da manyan kwamandojin Boko Haram 13 da ake nema ruwa a jallo.

DSS sun kama masu garkuwa da mutane da kuma likitan Boko Haram a wata jihar Arewa
DSS sun kama masu garkuwa da mutane da kuma likitan Boko Haram a wata jihar Arewa
Asali: Depositphotos

Afunanya ya kuma bayyana cewa a ranar 7 ga watan Nuwamba a Mararaban-Jos, karamar hukumar Igabi sun kama wani mai garkuwa da mutane Muhammad Musa.

Ya kara da cewa an kama wani Dare Okunwola, tare da abokan aikinsa Kim Dung (mai kera bindigar AK 47 na gargajiya), Hubert Akubulo, Chidi Ezubebem da kuma Elochukwu Oguabia.

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Za’a yi zaben gwamna, da na majalisar jiha a ranar 2 ga watan Maris - INEC

Yace an kuma kwato harsasai 1163 daga hannun su. Yace ana nan ana nema wasu yan kungiyar biyu, Bitrus Badung da Emeka Obi.

Ya kara da cewa a ranar 13 ga watan Nuwamba a Rafin Guzza, jihar Kaduna an kama wani Umar Nuhu na kungiyar ISWA kuma makusancin Liman Maitukwane (shugaban kungiyar Ansaru na yanzu).

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng