Sauya sunayen 'yan takara: APC a Niger sun fusata, sun sha alwashin daukar mataki
- Reshen jam'iyyar APC na Niger ta Gabas sun sha alwashin daukar mataki kan sauya sunayen 'yan takara da aka yi a shiyyar
- Uwar jam'iyyar ta kasa ta baiwa sanata mai ci, David Umaru tikitin takara, maimakon Alhaji Sani Musa (313) wanda ya lashe zaben fitar da gwanin da aka kammala
- Sun ce ba zata yiyu ace APC ta doke su kuma ta hana su kuka ba, don haka ba zasu janye wannan karar ba, zasu tabbata sun kaita karshe
Rikicin da ke ruruwa a cikin jam'iyyar APC a jihar Niger dangane da sakamakon zaben dan takarar majalisun tarayya a zaben 2019 ya wuce tunanin mutane, sakamakon yadda reshen jam'iyyar na Niger ta Gabas suka sha alwashin daukar mataki kan sauya sunayen 'yan takara da aka yi a shiyyar.
Uwar jam'iyyar ta kasa ta baiwa sanata mai ci, David Umaru tikitin takara na kai tsaye, maimakon Alhaji Sani Musa (313) wanda ya lashe zaben fitar da gwanin da aka kammala a mazabar watanni biyu da suka gabata.
Kungiyar yakin zaben Sani Musa a kujerar majalisar dattijai ta mazabar, sun sha alwashin ci gaba da bin diddigin wannan lamari akan Sanata Umaru a babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Abuja, inda suke kalubalantar yadda aka sauya sunan dan takararsu da sunan Sanata David Umaru.
KARANTA WANNAN: Dilolin miyagun kwayoyi sun afka kogin Niger a kokarinsu na tserewa jami'an NDLEA

Asali: Twitter
Darakta Janar na kungiyar yakin zaben, Alhaji Idris Abubakar Azozo, a zantawarsa da manema labarai a ranar Laraba a Minna, ya ce: "Zamu sake gabatar da kararmu gaban kotu a zaman da zata sake yi a ranar 3 ga watan Disamba, inda zamu bukaci kotu ta dakatar da David daga yayata kansa a matsayin dan takarar sanatan APC na mazabar Niger ta Gabas.
"Haka zalika zamu bukaci kotu ta gaggauta sauraron karar duba da muhimmancin shari'ar."
Da aka tambayeshi dalilin da ya sa kungiyar yakin zaben taki amincewa da hukuncin uwar jam'iyyar na kasa na cewar duk wadanda suka shigar da jam'iyyar kara su janye, Azozo ya ce: "Wannan umurnin na uwar jam'iyyar ya zo a makararran lokaci.
"Ba za ka doki yaro kuma ka hana shi kuka ba, hakan ba mai yiyuwa bane. Ba zamu janye wannan karar ba, zamu tabbata har mun kaita karshe."
Ya ce: "Idan har dan takararmu ya fadi a kotu, to zamu dauki hakuri mu yiwa jam'iyya aiki. Babu wani aibu a komawa kotu."
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng