Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa ya koma APC a jihar Bauchi

Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa ya koma APC a jihar Bauchi

Daya daga cikin 'yan takarkarin kujerar gwamnan jihar Bauchi dake a Arewa maso gabashin Najeriya a jam'iyyar adawa ta New Nigerian People’s Party (NNPP) mai suna Dakta Sama'ila Dahuwa ya koma jam'iyya mai mulki ta All Progressives Congress (APC).

Da yake bayyana dalilin sa na yin hakan, Dakta Sama'ila ya kira taron manema labarai inda a wurin ya bayyana cewa rashin sanin inda aka dosa a jam'iyyar ta sa ta da ne musabbabin dalilin komar sa APC din.

Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa ya koma APC a jihar Bauchi
Dan takarar gwamna a jam'iyyar adawa ya koma APC a jihar Bauchi
Asali: UGC

KU KARANTA: Najeriya ta zargi kungiyar kasashen yamma da taimakawa su Shekau

Legit.ng Hausa ta kuma samu cewa Dakta Sama'ila din ya tabbatar da zai yi iya bakin kokarin sa wajen ganin jam'iyyar ta APC ta samu nasara a dukkan zabukan da zata shiga a zabukan 2019.

A wani labarin kuma, Mataimaki na musamman ga shugaban kasar Najeriya a kan harkokin shari'a Mista Okoi Obono-Obla ya rubutawa jami'an 'yan sandan farin kaya watau Department of State Services (DSS) da kuma 'yan sandan Najeriya yana kalubalantar wani fasto da laifin yada karairayin mutuwar shugaba Buhammadu Buhari.

Takardun koken da fadar ta shugaban kasa ta rubuta ga jami'an tsaron da kuma majiyar mu ta samu sun nuna cewa an tura su ne a farkon watan nan inda a ciki aka bukaci su binciki wani Bishop Eze Orieka akan zargin yada karairayi akan shugaban kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel