Buhari na maimata zunubban da Obasanjo da Jonathan suka tafka - Ezekwesili
Daya daga cikin 'yan takarar kujerar shugabancin kasar Najeriya a jam'iyyar adawa ta Allied Congress Party of Nigeria (ACPN) Dakta Oby Ezekwesili, ta bayyana rashin jin dadin ta game da yadda tace shugaba Buhari yana yiwa kasar nan rikon sakainar kashi.
Haka zalika 'yar takarar shugaban kasar wadda tsohuwar minista ce a gwamnatin Cif Olusegun Obasanjo, ta yi ikirarin cewa kusan a iya dukkan kuskuren da tsaffin shugabannin kasar Najeriya suka tafka a lokacin mulkin su, shima Buhari yabi sahun su yana maimaitawa.

Asali: UGC
KU KARANTA: Barayin zaune: An kama yan kayan nauyi a filin jirgi
Legit.ng Hausa ta samu cewa Dakta Ezekwesili ta kara da cewa yanzu kasar tana bukatar shugaba ne mai hangen nesa da zai iya hada kan kasa domin ya kai al'ummar ta akan tudu abun da tace hakan ba zai samu ba a karkashin shugabancin na Buhari.
A wani labarin kuma, Rundunar jami'an tsaron Najeriya ta zargi kungiyar nan ta kasashen yamma dake rajin kare hakkin bi'adama ta Amnesty International a turance da taimakwa 'yan ta'addan Najeriya tare da kawo tarnaki ga rundunar don ganin bata yi nasara ba a kan su.
Rundunar haka zalika ta zargi kungiyar da sake maida hannun agogo baya musamman ma wajen zaliko wasu alkaluman abubuwan da suka faru a shekarun baya duk domin dakushe kokarin da rundunar take yi a yanzu.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng