Ainahin dalilan da su ka sa na fadi zaben 2015 – Goodluck Jonathan
Tsohon Shugaban Kasa, Dr Goodluck Jonathan, ya bayyana wasu kwararan dalilai da suka sanya shi faduwa a zaben 2015, ina Shugan Kasa Muhammadu Buhari na jam’iyyar All Progressives Congress (APC) ya yi nasara a kan sa.
A cewar Jonathan hadama da dogon buri na wasu gwamnonin PDP da suka sauya sheka zuwa jam’iyya mai mulki a yanzu wato APC, da yadda aka rika watsa labaran karya a kan sa da gwamnatin sa ne suka sanya shi faduwa a zaben 2015.
Jonathan ya yi wadannan ikirari a cikin wani littafin sa da ya kaddamar a yau Talata, 20 ga watan Nuwamba mai taken “My Transition Hours”, wanda a yanzu haka ana kan kaddamar shi a birnin tarayya.

Asali: Depositphotos
Ya kuma dora laifin faduwar sa zabe akan wasu manyan ‘yan Arewa wadanda suka so mulki ya koma a Arewa ta halin ko yaya, cewa sun kitsa masa munakisa domin hana shi yin tazarce.
KU KARANTA KUMA: 2019: Ingila ta shawarci Saraki, Dogara da sauransu kan sakaci da aikinsu
Jonathan ya kara da cewa duk da gudun kaddarar da yawancin gwamnonin da suka koma APC daga PDP suka yi, hakan bai hana a yanzu sai ga shi ana cin mutuncin su da tazarta su a cikin gwamnatin APC din da suka taimaka aka kafa.
Ya ce tuni dama wasu shugabannin Arewa na kungiyoyin dattawan yankin suka nemi hana shi zama shugaban kasa wanda dokar Najeriya ce ta ba shi wannan damar zama, a bayan babu ran tsohon shugaban kasa Umaru Yar’Adua a cikin 2010.
Jonathan ya ce duk da irin wannan barazana da suka rika nuna masa da kuma kaifin adawa, sai da ya yi nasara a zaben 2011.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng