Karancin albashi: N30,000 bai yi yawa ba don haka ku biya – Sanata Ndume

Karancin albashi: N30,000 bai yi yawa ba don haka ku biya – Sanata Ndume

Sanata Ali Ndume, mai wakiltan yankin Borno ta kudu a ranar Talata, 20 ga watan Nuwamba ya goyi bayan bukatar kungiyar kwadago na biyan N30,000 a matsayin albashi mafi karanci.

Ndume ya bayyana ra’ayinsa ga kamfanin dillancin labaran Najeriya (NAN) a babbar birnin tarayya Abuja.

Da yake watsi da adawar da gwamnonin jiha ke yi akan wannan bukata, ya bayyana cewa N30,000 bai yi yawa ba kuma ya kamata a amince da hakan sannan a fara biya ba tare da bata lokaci ba.

Karancin albashi: N30,000 bai yi yawa ba don haka ku biya – Sanata Ndume
Karancin albashi: N30,000 bai yi yawa ba don haka ku biya – Sanata Ndume
Asali: UGC

"A gani na, N30,000 a matsayin mafi karancin albashi bai yi yawa ba sannan ya kamata ace an amince da hakan harma a fara biya.

KUKARANTA KUMA: 2019: Ingila ta shawarci Saraki, Dogara da sauransu kan sakaci da aikinsu

“Ya kamata a dunga duba mafi karancin albashin yan Najeriya, doka mata baarcewa a dunga duba ga hakan bayan kowani shekara biyar.

“idan gwamnoni suka ce kawai ba za su iya biya ba, ina da ja akan haka.

“Idan ba za ka iya biya ba toh ta yaya kuma dalili? Na dauka za’a kawo wani kwakwaran hujja ta gaskiya.”

Ndume ya bayyana cewa shi a ganinsa ma kamata yayi ace mafi karancin albashi ya kai N40,000.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng