Buhari ya gwammaci ace ya fadi maimakon yin magudi a zaben 2019 – Femi Adesina

Buhari ya gwammaci ace ya fadi maimakon yin magudi a zaben 2019 – Femi Adesina

Femi Adesina, babban mai ba shugaban kasa shawara a kafofin watsa labarai, ya bayyana cewa Shugaban Kasa Muhammadu Buhari ya gwammaci ace ya fadi zabe maimakon yin magudi a zaben 2019.

Kakakin shugaban kasar ya bayyana hakan ne a loacin wani shiri na talbijin din ARISE TV a ranar Talata, 20 ga watan Nuwamba.

Da yake sharhi akan aben 2019, Adesna yace babu makawa tsarin zzai zamo na gaskiya da amana.

Buhari ya gwammaci ace ya fadi maimakon yin magudi a zaben 2019 – Femi Adesina
Buhari ya gwammaci ace ya fadi maimakon yin magudi a zaben 2019 – Femi Adesina
Asali: Depositphotos

“Na yi mamaki kan cewa wannan shugaban kasa na tare da ku tsawon shekaru uku da rabi amma ba ku san abunda ai iya yi ba,” inji shi.

“Idan har wani zai yi magudin zabe toh ba shugaban kasa Muhammadu Buhari ba ne. Zai gwammaci ace ya fadi zabe.”

KU KARANTA KUMA: Ku yi hakuri kudin TraderMoni zai iso wurin yan Najeriya da dama – Osinbajo ga yan kasuwa

Da yake martani aka furucin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) na cewa takardar Buhari na ‘Next Level’ ya gaza kawo wani mafita Adesina yace: “PDP a kasa take kuma za ta ci gaba da kasancewa a haka don haka ba zan bata lokaci wajen yin Magana a kansu ba.”

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng