Sojoji da dama sun mutu, dozin sun jikkata a harin da Boko Haram ta kai Borno
- Harin da mayakan Boko Haram suka kai sansanin soji da ke jihar Borno, ya yi sanadin lakume rayukan sojoji da dama da kuma jikkata wasu
- Lamarin ya faru ne a wani kauyen Matele, da ke makwaftaka da kogin Chadi, da misalin karfe 5:00 na yamma
- Wata majiya daga rundunar sojin ya ce mayakan na Boko Haram sun mamaye sojojin tare da fin karfinsu, inda suka samu nasarar kwashe kusan gaba daya makamansu
Sojoji da dama ne suka gamu da ajalinsu, yayin da dozin daga cikinsu suka samu raunukan harsasai, a lokacin da mayakan Boko Haram suka kai wani mummunan hari a sansanin soji da ke karamar hukumar Matele, jihar Borno, a yammacin ranar Lahadi.
Lamarin ya faru ne a wani kauyen Matele, da ke makwaftaka da kogin Chadi, da misalin karfe 5:00 na yamma.
Wata majiya daga rundunar sojin ya ce mayakan na Boko Haram sun mamaye sojojin tare da fin karfinsu, inda suka samu nasarar kwashe kusan gaba daya makamansu.
KARANTA WANNAN: APC ta yi barazanar korar wasu jiga jigan jam'iyyar da ke son bata matsala a zaben 2019

Source: Depositphotos
"Sun bude wuta da kuma bude kofar shiga cikin sansanin da karfin tsiya, mun rasa sojoji da dama wadanda suka tsaya tsayin daka don hana 'yan ta'addan shiga, yayin da wasu har yanzu basu dawo ba. Daga bayanan da nike da su, 'yan ta'addan sun fi sojojin yawa, kuma sun fi karfinsu.
"Hakika wannan ranar bakin ciki ce a garemu, 'yan ta'addan sun yi amfani da wata 'yar dama ce suka far mana, lamarin ya munana a bangaren jami'an sojin," a cewar majyar.
Wani babban jami'i, wanda ya bukaci a sakaya sunansa, ya tabbatar da kai harin, inda ya ce, "Mun samu rahoton cewa Boko Haram ta kai hari a kauyen Matele, a karamar hukumar Kukawa, a ranar Lahadi, harin ya shafe awanni, inda suka samu nasarar kutsawa cikin sansanin, yanzu, sai dai labari kawai.
"Damuwar yanzu ba zata wuce yadda 'yan ta'addan kullum ke kara karfi ba kuma suna kara hada muggan kayan yaki a kusan kowanne sati, ya zama wajibi rundunar soji ta tashi tsaya akan hakan, dole a kara samar da yawan sojoji da kuma kwararan bayanai don kawo karshen 'yan ta'addan," a cewar jami'in.
Haka zalika, a ranar Juma'a, rahotanni sun bayyana cewa, yan ta'addan sun kai wani sabon hari a kauyen Kekeno da ke karamar hukumar Kukawa, inda suka kashe mutane da dama.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng