Masu garkuwa da mutane sun sace mutum 45 a Zamfara
Rahotanni sun kawo cewa, masu garkuwa da mutane sun yi gaba da mutum 45wadanda suka hada da yara, da mata a karamar hukumar Shinkafi da ke jihar Zamfara.
Satar mutanen ya afku ne tsakanin ranar Alhamis zuwa Asabar.
Da farko dai a safiyar ranar Alhamis masu garkuwar a kan hanyar garin Kware zuwa garin Shinkafi sun yi awon gaba da wata mota dake dauke da mutane 35 a kan hanyarsu ta zuwa cin kasuwa a garin na Shinkafi.
A cewar wani majiya da ya nemi a boye sunansa, ya bayyana cewa, dukan mutane 35 sun fada hannun masu garkuwar ne a lokacin da suke kokarin fito da motarsu bayan da ta kame a cikin yashi.

Asali: Depositphotos
Daga nan ne suka ga ‘yan ta’addan sun fito su da yawa a kan mashina dauke da muggan makamai, inda suka zagaye su sannan kuma suka yi awon gaba da su.
An kuma ruwaito cewa, haka kuma a ranar Asabar, a yi sace mutum 11 ciki har da mace daya a kuyen Kware duk dai a cikin karamar hukumar Shinkafi, bayanai sun kuma nuna cewa an kashe mutum daya a lokacin da aka kawo harin.
Jami’in hulda da jama’a na rundunar ‘yan sandan jihar SP Mohammed Shehu ya tabbatar da faruwa lamarin, ya ce, tuni a kan tura wata kakkarfar runduna ‘yan sanda don shawo kan wanna lamarin a karamar hukumar Shinkafi.
KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Yan sanda da mutanen unguwa sun dakile wani fashin banki a Ile-Ife
Ya kuma kara da cewa, a halin yanzu dukkan bangarorin jami’an tsaron jihar ciki har da sojoji sun shirya gudanar da ayyukan fatattakar ‘yan ta’adda daga dukan maboyarsu.
Daga karshe ya ce ‘yan sanda za su yi dukkan abin da ya kamata don ganin an cafke ‘yan ta’addan gaba daya tare da kuma hukunta su.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Asali: Legit.ng