Cikin hotuna: An shiga filin daga, Buhari ya kaddamar yakin neman zaben 2019

Cikin hotuna: An shiga filin daga, Buhari ya kaddamar yakin neman zaben 2019

Shugaba Muhammadu Buhari ya kaddamar da yakin neman zaben kujeran shugaban kasa a zaben 2019 a yau Lahadi, 18 ga watan Nuwamba, 2018 a farfajiyar taro na fadar shugaban kasa.

Shugaban kasan ya yi kira ga yan siyasa da su gudanar da yakin neman zabe da zaman lafiya kuma kada su birkita kasa.

Buhari ya ce gwamnatinsa ta samu nasarori daban-daban cikin shekaru ukun da tayi kuma tana sa ran cigaba da hakan idan aka zabe shi.

Cikin hotuna: An shiga filin daga, Buhari ya kaddamar yakin neman zaben 2019
Cikin hotuna: An shiga filin daga, Buhari ya kaddamar yakin neman zaben 2019
Asali: Twitter

Yace: "Ina sane cewa an fara yakin neman zaben majalisar dokokin tarayya da na shugaban kasa a yau, ina kira ga yan takara su gudanar yakin neman cikin zaman lafiya,"

"Bamu da wata kasa face Najeriya, ba zamu banka mata wuta ba saboda siyasa."

KU KARANTA: Kada ku zabi APC, Atiku ya bukaci jama’ar yankin Arewa maso gabas

Cikin hotuna: An shiga filin daga, Buhari ya kaddamar yakin neman zaben 2019
Cikin hotuna: An shiga filin daga, Buhari ya kaddamar yakin neman zaben 2019
Asali: Facebook

Mun kawo muku rahoton cewa shugaba Muhammadu Buhari zai bayyana yadda yakin neman zabensa zai kasannce da taken ‘Next Level’ tsakanin karfe 5 zuwa karfe 8 a fadar shugaban kasa Abuja.

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta wato INEC ta baiwa jam’iyyun siyasa daman fara yakin neman zaben shugaban kasa da yan majalisan dokokin tarayya daga Yau Lahadi, 18 ga watan Nuwamba 2018.

Kakakin kwamitin yakin neman zaben shugaba Muhammadu Buhari, Festus Keyamo, ya ce wannan takarda da Buhari zai gabatar na daga cikin takardu guda biyu da bayyana domin fara yakin neman zaben.

Cikin hotuna: An shiga filin daga, Buhari ya kaddamar yakin neman zaben 2019
Cikin hotuna: An shiga filin daga, Buhari ya kaddamar yakin neman zaben 2019
Asali: Twitter

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng