Kotu tayi yanke hukunci akan wata kungiyar 'yan madigo a Abuja
Wata kotu dake zaman ta a garin Abuja mallakar gwamnatin tarayya ta kori karar da wata kungiyar 'yan madigo ta shigar a gaban ta suna kalubalantar hana su satifiket da hukumar yiwa kungiyoyi da kamfuna rijista watau Corporate Affairs Commission (CAC) a turance ta ki yi masu.
A zauren kotun, Mai shari'a Nnamdi Dimgba, ya bayyana cewa matakin da hukumar ta CAC ta dauka na kin yi mau rijista yayi daidai da dokokin da suka kafa hukumar musamman ma na sashe na 30 (1) (c) a kundin dokar da ta kafa ta na 2004.

Asali: Twitter
KU KARANTA: Matasa sun yiwa Atiku Abubakar alkawarin kuri'a miliyan 10
Legit.ng Hausa ta samu cewa tun farko dai wata babbar shakiyyiya ce mai suna Pamela Adie ta shigar da karar biyo bayan kin yiwa kungiyar ta ta 'yan madigo da kare hakkin su da ta sawa suna “Le3bian Equality and Empowerment Initiatives” da turanci rijista da hukumar ta CAC tayi.
A wani labarin kuma, Hankula sun tashi a garin Awka, babban birnin jihar Anambra yayin da aka kama wani matashi mai shekaru 19 kacal a duniya mau suna Sunday Owo da ya ziyarci wata asibitin gargajiya da sassan jikin mutane da kuma kwalba cike da jini kulle a cikin buhu.
Kamar yadda muka samu, matashin ya fito ne daga karamar hukumar Ohaukwu ne ta jihar Ebonyi dake makwaftaka da jihar ta Anambra kuma kamar yadda yace, ya zo ne neman maganin yin kudi ko ta halin ka-ka.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng