Fadan manya: Gwamnan Osun da Obasanjo sun samu sabani game da sha'anin mulki
Gwamnan jihar Osun dake a shiyyar kudu maso yammacin Najeriya mai barin gado Mista Rauf Aregbesola a ranar Asabar din da ta gabata ya samu sabani da tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo game da sha'anin mulkin tafiyar da kananan hukumomi.
Shi dai tun farko tsohon shugaban kasar Najeriya Cif Olusegun Obasanjo a wata fira da yayi da manema labarai ya bayyana cewa gwamnonin jahohin Najeriya ne ke hana samar da kananan hukumomi masu cin gashin kan su a matsayin bangare daya na gwamnati.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Sojoji sun halaka wasu 'yan kunar bakin wake
Legit.ng Hausa ta samu cewa sai dai da yake maida martani game da hakan, Gwamnan na Osun ya ce ko kusa ikirarin tsohon shugaban kasar ba gaskiya bane domin a cewar sa dukkan inda ake bin tsarin mulki na tarayya to daman ba bu kananan hukumomi.
Haka zalika ya kara da cewa kuma ma ai shi tsohon shugaban kasar shaida ne na cewa bai kamata a bar kananan hukumomi su tsaya da kafafun su ba domin kuwa tsare-tsaren da gwamnatin sa ta kawo a lokacin yana mulki na samar da lafiya a matakin farko duk bai yi nasara ba.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng