Da duminsa: Daga karshe, an maye sunan Mannir Dan’iya da gwamna Aminu Tambuwal

Da duminsa: Daga karshe, an maye sunan Mannir Dan’iya da gwamna Aminu Tambuwal

Hukumar gudanar da zabe ta kasa mai zaman kanta ta tabbatar da gwamnan jihar Sokoto, Aminu Waziri Tambuwal, a matsayin dan takaran gwamnan jihar na zaben bana karkashin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP).

Game da cewar jaridar New Telegraph, kwamishanan hukumar INEC kan ilimantar da msu zabe, Festus Okoye, ne ya tabbatar da hakan.

A kwanakin baya da hukumar ta saki jerin sunayen yan takara, an nemi sunan gwamna Aminu Waziri Tambuwal an rasa.

Okoye yace: “Jam’iyyar PDP tayi amfani da lokacin da hukumar ta bada na daman iya sauya sunan dan takara wajen sanya sunan Tambuwal.”

“Kamar yadda kuka sani, dokar zabe ta bayyana cewa kowani dan takaran da jam’iyyar ta zaba na iy janye takararsa ta hanyar rubutawa hukumar wasika wanda ya sanya hannu kuma ya kai ofishin jam’iyyar da ta zabeshi.”

A jiya, jam’iyyar PDP ta yi wannan sauyin dan takaran gwamnan jihar Sokoto. Sun sanya sunan Aminu Waziri Tambuwal matsayin dan takara.”

KU KARANTA: Babu adalci da sanin ya kamata a PDP - Gwamnan jam'iyyar

Gwamna Tambuwal ya sha kasa hannun tsohon mataimakin shugaban kasa, Atiku Abubakar, a zaben fidda gwanin shugaban kasar karkashin jam’iyyar PDP.

A ranan Laraba, mataimakin gwamnan jihar Ahmed Sokoto, ya yi murabus daga kujerarsa.

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel