Yanzu-yanzu: An saki yan biyun Zamfara

Yanzu-yanzu: An saki yan biyun Zamfara

Labaran da shigo mana yanzunnan na nuna cewa an saki yan mata tagwayen da akayi garkuwa da su a jihar Zamfara da yammacin yau Asabar, 17 ga watan Nuwamba, 2018.

Yanzu-yanzu: An saki yan biyun Zamfara
Yanzu-yanzu: An saki yan biyun Zamfara
Asali: Facebook

A kwanakin baya, gungun miyagun mutane yan bindiga da suka yi garkuwa da wasu yan mata tagwayen sun bayyana cewa zasu kashe tagwayen matukar ba’a biya musu bukatarsu na biyan kudin fansa ba.

Legit.com ta ruwaito wani ma’abocin kafar sadarwar zamani ta Facebook, Zaidu Bala ne ya tabbatar da haka kamar yadda ya bayyana a shafinsa na Facebook, inda yace yan bindigan sun dauki alwashin kashe guda daga cikin yan matan su bar daya.

KU KARANTA: Zaben 2019: Atiku ya samu karbuwa a wajen Inyamurai, APC ta ji haushi

Da wannan majiyarmu ke kira da babban murya ga shugaban kasa Muhammadu Buhari da gwamnan jahar Zamfara Abdul Aziz Yari da suyi duk mai yiwuwa don taimaka ma iyayen tagwayen nan ta hanyar cetosu da ransu.

Idan za’a tuna a ranar 25 ga watan Oktoba ne aka samu rahoton sace yan matan da wata gungun masu garkuwa da mutane suka yi a lokacin da suke kan hanyar raba ma yan uwansu da kawayensu ankon bikinsu wanda ake gab da gudanar da bikin.

An sace yan matan ne a karamar hukumar Zurmi ta jahar Zamfara, kamar yadda mataimakin shugaban hukumar Abubakar Muhammad ya bayyana, inda yace an sace mutane bakwai a cikin kwanaki biyu, daga cikinsu har da tagwayen.

Ku biyo mu a https://facebook.com/legitnghausa

ko a http://twitter.com/legitcomhausa

KU LATSA: Hanyar sauko da sabuwar manhajar jaridar Legit.com Hausa cikin sauki

Ga masu shawara ko korafi, a same mu a labaranhausa@corp.legit.com

Sanarwa na musamman: Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel