Gara shegen kowa da na budurwa - Shugaba Buhari ya aike da sako zuwa ga PDP

Gara shegen kowa da na budurwa - Shugaba Buhari ya aike da sako zuwa ga PDP

Shugaban kasar tarayyar Najeriya, Muhammadu Buhari ya sha alwashin cewa shifa sai inda karfin sa ya kare amma da yardar Allah jam'iyyar Peoples Democratic Party, (PDP) ba zata dawo kan mulki ba a Najeriya.

Shugaba Buhari din ya bayyana hakan ne lokacin da ya karbi bakuncin wasu shugabannin 'yan kabilar Ibo a fadar sa, ranar Juma'ar da ta gabata inda yace jam'iyyar ta PDP ba karamar ta'asa tayi wa kasar ba.

Gara shegen kowa da na budurwa - Shugaba Buhari ya aike da sako zuwa ga PDP
Gara shegen kowa da na budurwa - Shugaba Buhari ya aike da sako zuwa ga PDP
Asali: UGC

KU KARANTA: Buratai ya sha alwashin cigaba da yiwa Buhari biyayya

Legit.ng Hausa ta samu cewa shugaban kasar ya kara da cewa shi fa ya kwammace kowa ma ya mulki kasar nan amma fa banda jam'iyyar PDP domin a cewar sa sune suka kashe kasar cikin shekaru 16 da sukayi suna mulki duk kuwa da irin makudan kudaden da suka samu.

A wani labarin kuma, Kunngiyar gamayyar hadakar cigaban 'yan kabilar Yarbawa watau Oodua Peoples Congress, OPC, ta bayyana cewa ita fa har yanzu bata gama yanke shawarar wanda za su zaba ba a matsayin shugaban kasa a zaben 2019.

Sai dai kungiyar kuma ta bayyana cewa abun da take da yakini kanshi dai shine cewa zata goyawa dukkan wanda ya yarda da manufofin ta ya kuma amince zai sauya fasalin kasa a zaben mai zuwa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel