Da duminsa: Rundunar soji da taimakon manoma sun fatattaki mayakan Boko Haram a Borno
Dakarun sojin kasa na bataliya ta 222 da ke Konduga, jihar Borno, tare da taimakon manoma, sun gudanar da wani aiki akan hanyar garin Mushari zuwa Galtimari, inda suka samu nasarar fatattakar mayakan Boko Haram da suka zo satar Albasa sa sauran kayan amfanin gona.
Bayanin hakan na kunshe ne a cikin wata sanarwa da shelkwatar rundunar sojin ta fitar a shafinta na Twitter, inda ta bayyana cewa, a yayin sumamen, dakarun sun samu nasarar kwantar da daya daga cikin mayakan Boko Haram, tare da kwace kayayyakinnda suka sace, da kuma kekunan da suka zo da su.
KARANTA WANNAN: APC ta fara fuskantar matsala tun bayan ficewar Saraki daga jam'iyyar - Chief Ebenezer Babatope

Source: UGC
Wannan na daga cikin yunkurin da rundunar sojin ke yi na ganin ta kawo karshen ta'addancin a yankunan Arewa maso gabashin kasar, musamman ma kakkabe ragowar mayakan Boko Haram daga shiyyar, don wanzar da zaman lafiya.
KARANTA WANNAN: Karuwai a jihar Kaduna sun jinjinawa El-Rufai bisa janye dokar ta baci a lokutan dare

Source: UGC
A wani labarin makamancin wannan kuwa, dakarun rundunar Sojan Najeriya tare da hadin gwiwar kungiyar jaruman matasan jahar Borno wanda aka fi sani da suna Civilian JTF sun yi ma mayakan Boko Haram rakiyan kura bayan wani hari da suka kai a kauyen Mammanti na jahar Borno.
Legit.com ta ruwaito hadakan Sojojin sun afka cikin dazukan da mayakan na Boko Haram ke samun mafaka tare da taimakon mafarautan yankin, a kokarinsu na kakkabe ragowar yan ta’addan Boko Haram dake kai hare hare a yankin.
Shelkwatar rundunar Sojan kasa ta sanar da cewa Sojojin sun ratsa kauyuka da dama a wannan samame da suka kai, da suka hada da Kamari, Koyamti, Durwala, Ajiri, da Tumballa, inda suka tabbatar sun kakkabe duk wani dan Boko Haram dake fakewa a kauyukan.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng