APC ta fara fuskantar matsala tun bayan ficewar Saraki daga jam'iyyar - Chief Ebenezer Babatope

APC ta fara fuskantar matsala tun bayan ficewar Saraki daga jam'iyyar - Chief Ebenezer Babatope

- Chief Ebenezer Babatope, ya bayyana cewa, APC ta tafka babban kuskure, na budewa shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki kofa, har ya fice daga jam'iyyar

- Mamban kwamitin amintattun ya kuma tariyo yadda ya gargadi APC tun a lokutan baya, da jita jita ta fara yawo na cewar Saraki zai bar jam'iyyar

- Ya ce a duk lokacin da ka kitsa makirci wa Saraki, to ka sani yana sane da kai, kuma shi tuni ya dauki matakai na dakile duk wani shirinka, kana tunani daya ne, shi yana yin biyu

Wani mamba a hukumar amintattu na jam'iyyar PDP, Chief Ebenezer Babatope, a cikin wata hira da yayi da jaridar Punch, ya bayyana cewa, jam'iyyar APC ta tafka babban kuskure, na budewa shugaban majalisar dattijai, Bukola Saraki hanya, har ya fice daga jam'iyyar.

Chief Ebenezer Babatope, ya ce duk da cewa a lokacin da ita ma APC ke kwacewa PDP mambobinta, ba su samu damar yin katabus ba, kuma a lokacin da suka nuna sha'awar dawowa jam'iyyar, sun yi maraba da su, to sai dai barin mutum kamar Saraki ya fice daga jam'iyya ba karamin kuskure bane.

Ya ce, "Misali, mutum kamar Saraki na da karfi fiye da tunanin mutane; har yanzu na kasa gane dalilin da ya sa APC ta barshi har ya fice daga jam'iyyar. Ba shi ba, mahaifinsa, Dr. Olusola Saraki, mutum ne da ya shahara ainun. Mahaifinsa ne ya jajurce har sai da ya tabbatar Sanata Cornelius Adebayo ya zama gwamna a wancan lokacin."

KARANTA WANNAN: Tambuwal ya gargadi magoya bayan jam'iyyar PDP da su kauracewa yin gulma da tsugudidi

APC ta fara fuskantar matsala tun bayan ficewar Saraki daga jam'iyyar - Chief Ebenezer Babatope
APC ta fara fuskantar matsala tun bayan ficewar Saraki daga jam'iyyar - Chief Ebenezer Babatope
Asali: Twitter

Mamban kwamitin amintattun ya kuma tariyo yadda ya gargadi APC tun a lokutan baya, da jita jita ta fara yawo na cewar Saraki zai bar jam'iyyar, "a lokacin na gargadi APC akan ta yi taka tsan-tsan da irin rikon sakainar kashin da take yiwa Saraki. Saboda shi gawurtacce ne a fagen siyasa.

"Lokacin da zai bar APC, munate na cewa ai haka yafi, suna zaginsa suna aibata shi, da kiransa munanan sunaye, amma kaga mu a PDP, sai muka yi maraba da shi, muka yi murnar sake kasancewa a inuwa daya da shi. Ko ba komai, mahaifinsa abokina ne kuma na yi masa farin sani."

Ko da aka tambayi Chief Babatope, kan zarge zargen da ake yi na takun saka tsakanin shugaban jam'iyyar APC na kasa, Adams Oshiomhole, da Saraki, sai cewa yayi: "Na san cewa dai Oshiomhole ya yaudari kansa. A duk lokacin da ka kitsa makirci wa Saraki, to ka sani yana sane da kai, kuma shi tuni ya dauki matakai na dakile duk wani shirinka, kana tunani daya ne, shi Saraki na yin biyu."

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng