Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar Talata a matsayin hutu

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar Talata a matsayin hutu

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar Talata, 20 ga watan Nuwamba a matsayin ranar hutu domin bikin tunawa a ranar haihuwar fiyayyen halitta Annabi Muhammad SAW wato Eid-El Maulud.

Ministan cikin gida, Laftanal Janar Abdulrahman Dambazau ne ya bayyana hakan a madadin gwamnatin tarayya.

A wata sanarwa dauke da sa hannun sakataren din-din na ma’aikaar cikin gida ya bukaci Musulmai da su yi koyi da koyarwar fiyayyen halitta wanda suka hada da sadaka, tausayi, hakuri da kuma zaman lafiya da sauran ayyukan alkhairi.

Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar Talata a matsayin hutu
Gwamnatin tarayya ta kaddamar da ranar Talata a matsayin hutu
Asali: Facebook

KU KARANTA KUMA: Yanzu Yanzu: Gobara ta lashe yan gida daya su 4, da wani mutun guda a Kebbi

Yayinda yake kira ga dukkanin yan Najeriya da su yi koyi ga hakan tare da bayar da hadin kai wajen kawo kashen kalubalen da kasar ke fuskanta, Dambazau ya bayar da tabbacin cewa gwamnatin tarayya na ci gaba da jajircewa waje ganin hadin kan kasar.

Sannan kuma cewa za’a tabbatar da zabe na gaskiya da aminci.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ.com Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel