Yan Nigeria sun zuba idanu su ga matakin da Buhari zai dauka kan Oshiomhole - Saraki

Yan Nigeria sun zuba idanu su ga matakin da Buhari zai dauka kan Oshiomhole - Saraki

- Bukola Saraki ya ce 'yan Nigeria na ci gaba da zura idanu don ganin yadda shugaban kasa Buhari zai yanke hukunci kan zarge-zargen da ake yi Adams Oshiomhole

- Sai dai Oshiomhole ya bukaci Saraki da ya lissafa masa sunayen 'yan takarar da yake ikirarin ya karbi kudin daga wajensu ko kuma ya makashi kotu

- Saraki ya ce gazawar shugaban kasar na bin diddigin maganar zata kawo karshen wani tagomashinsa da kuma ce ce kuce na cewar yana yaki da cin hanci da rashawa

Shugaban majalisar dattijai Bukola Saraki ya ce 'yan Nigeria na ci gaba da zura idanu don ganin yadda shugaban kasa Muhammadu Buhari zai yanke hukunci kan zarge-zargen da ake yi Adams Oshiomhole, shugaban jam'iyyar APC na kasa.

Ya bayyana hakan a lokacin da ya ke mayar da martani kan barazanar da shugaban APC ya yi na cewar zai maka shi kotu.

A baya bayan nan ne Saraki ya ce shugaban jam'iyyar na APC, ba shi da sauran mutuncin da zai ci gaba da zama a cikin harkokin siyasa sakamakon irin zargin da wasu gwamnoni ke masa na karbar cin hanci daga wajensu a lokacin zaben fitar da gwani na jam'iyyar.

KARANTA WANNAN: Mutane 193,915 ne zasu kada kuri'a a zaben maye gurbi na jihar Katsina - INEC

Sai dai Oshiomhole ya bukaci Saraki da ya lissafa masa sunayen 'yan takarar da yake ikirarin ya karbi kudin daga wajensu ko kuma ya makashi kotu.

Bukola Saraki: Yan Nigeria sun zuba idanu su ga matsayar da Buhari zai dauka kan Oshiomhole
Bukola Saraki: Yan Nigeria sun zuba idanu su ga matsayar da Buhari zai dauka kan Oshiomhole
Asali: Facebook

A cikin wata sanar da aka bayar a ranar Alhamis, Yusuph Olaniyonu, mai baiwa Saraki shawara na musamman kan kafofin sadarwa, ya ruwaito shugaban majalisar na cewa a shirye yake ya kara da Oshiomhole a gaban kotu.

"Yan Nigeria na nan sun zuba idanu don ganin yadda shugaban kasar zai yanke hukunci kan manyan zargin da ake yiwa shugaban jam'iyyar ta APC," a cewar sa.

"Muna fatan shugaban kasar da shirinsa na yaki da cin hanci da rashawa, za su yi binciken kwakwaf kan wadannan zarge zarge da ake yiwa Oshiomhole.

"Gazawar shugaban kasar na bin diddigin maganar zata kawo karshen wani tagomashinsa da kuma ce ce kuce jam'iyyar na cewar suna yaki da cin hanci da rashawa. Ya kamata shugaban kasar ya bari a gudanar da kwakkwaran bincike. Wannan karon ba sauran boye-boye."

Rahotanni sun bayyana cewa hukumar tsaro ta DSS, ta fara tuhumar Oshiomhole kan wadannan zarge zarge da ake masa.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng