Mutane 193,915 ne zasu kada kuri'a a zaben maye gurbi na jihar Katsina - INEC

Mutane 193,915 ne zasu kada kuri'a a zaben maye gurbi na jihar Katsina - INEC

- INEC, ta ce za ta gudanar da sahihin zaben gurbi na mazabar Kankia/Ingawa/Kusada da ke jihar Katsina, wanda zai gudana ranar 17 ga watan Nuwamba, 2018

- Wannan tabbacin ya biyo bayan sanarwar da INEC ta bayar na cewar mutane 193,915 ne ke da rejista don kada kuri'a a zaben maye gurbin kujerar dan majalisar

- INEC ta ce, ma'aikatan hukumar guda 1,874, da suka hada da matasa masu yiwa kasa hidima NYSC, za su gudanar da aikin zaben a fadin kananan hukumomi 3 da abun ya shafa

Hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, ta kara baiwa 'yan Nigeria tabbacin cewa za ta gudanar da sahihin zabe wanda kowa zai gamsu da shi, a zaben maye gurbi na kujerar majalisar wakilai ta tarayya na mazabar Kankia/Ingawa/Kusada da ke jihar Katsina, wanda zai gudana ranar 17 ga watan Nuwamba, 2018.

Wannan tabbacin ya biyo bayan sanarwar da hukumar INEC ta bayar na cewar mutane 193,915 ne daga mazabar, ke da rejista don kada kuri'a a zaben maye gurbin kujerar dan majalisar.

Kwamishinan hukumar INEC na jihar, Ibrahim Zarewa, ya bayar da wannan tabbacin a waji taron masu ruwa da tsaki da ya gudana a garin Kankia a ranar Larabar da ta gabata, a fuskantar zaben ranar Asabar din mai zuwa.

KARANTA WANNAN: Rundunar soji na kan gabar kawo karshen ta'addancin Boko Haram a Arewa-maso-Gabas - Buratai

Mutane 193,915 ne zasu kada kuri'a a zaben maye gurbi na jihar Katsina - INEC
Mutane 193,915 ne zasu kada kuri'a a zaben maye gurbi na jihar Katsina - INEC
Asali: UGC

A cewar Zarewa, "INEC ta dukufa ainun wajen rike martabarta da kuma dokokinta na gudanar da sahihin zabe mai cike da inganci da gaskiya, wanda zai samu karbuwa a wajen kowa bayan an kammala shi."

Kwamishinan hukumar INEC din, ya kuma ce za a tantance masu kada kuri'a, tare da gudanar da zaben a akwatuna 357 da ke a mazabar, inda mutane 193,915 da akayiwa rejista ne za su kada zabensu a ranar.

Ya tabbatar da cewa, ma'aikatan hukumar guda 1,874, da suka hada da mambobin matasa masu yiwa kasa hidima NYSC, za su gudanar da aikin zaben a fadin kananan hukumomi 3 da abun ya shafa.

A daya bangaren kuwa, kakakin majalisar dokoki ta jihar Katsina, Abubakar Yahaya Kusada na jam'iyyar APC; Abdulsamad Abdullahi na jam'iyyar PDP; Nasiru Aminu na jam'iyyar PRP da kuma Abdullahi Umar na jam'iyyar YES, ne ke fafutukar ganin sun maye gurbin kujerar majalisar wakilan tarayyar.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng