Shugaban hukumar NEMA ya sake shiga wata sabuwar tsomomuwa

Shugaban hukumar NEMA ya sake shiga wata sabuwar tsomomuwa

Shugaban hukumar nan ta gwamnatin tarayyar Najeriya dake kula da bayar da agajin gaugawa watau National Emergency Management Agency (NEMA), mai suna Mustapha Maihaja, ya sake shiga wata sabuwar tsomomuwa.

Yanzu haka dai ana zargin shi ne da kulle-kullen boye shinkafar da aka zarge shi da karkatarwa.

Shugaban hukumar NEMA ya sake shiga wata sabuwar tsomomuwa
Shugaban hukumar NEMA ya sake shiga wata sabuwar tsomomuwa
Asali: Depositphotos

KU KARANTA: An gano alabshin gwamnoni a Najeriya

Mai karatu dai zai iya tuna cewa kimanin sati daya da ya gabat kwamitin sa' ido na majalisar tarayya ya bankado wata kullaliyar da shugaban hukumar ta NEMA ke yi na karkatar da shinkafar agaji da ta kai ton 6,779 ta 'yan gudun hijira da gwamnatin kasar Sin ta bayar taimako.

Legit.ng Hausa ta samu cewa sai dai yanzu 'yan majalisar sun bayyana cewa Mustapha Maihaja din tuni ya isa isa jihar Gombe a wani mataki na boye shinkafar tare da yin badda sawu domin kar a gane irin badakalar da ya aikata.

A wani labarin kuma, Hankula sun tashi a garin Awka, babban birnin jihar Anambra yayin da aka kama wani matashi mai shekaru 19 kacal a duniya mau suna Sunday Owo da ya ziyarci wata asibitin gargajiya da sassan jikin mutane da kuma kwalba cike da jini kulle a cikin buhu.

Kamar yadda muka samu, matashin ya fito ne daga karamar hukumar Ohaukwu ne ta jihar Ebonyi dake makwaftaka da jihar ta Anambra kuma kamar yadda yace, ya zo ne neman maganin yin kudi ko ta halin ka-ka.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng