Ruwa ya karewa dan kada: Hukumar EFCC tayi babban kame a wata jami'ar Najeriya
Hukumar gwamnatin tarayya dake yaki da masu yiwa tattalin arzikin kasa tu'annati watau Economic and Financial Crimes Commission (EFCC) ta sanar da samun nasarar cafke wasu hatsabiban dalibai da suka kware wajen zamba cikin aminci da damfara a kafafen sadarwar zamani da yanar gizo.
Daliban wadan da suka kai akalla 34 an kama su ne a wani gida mai lamba 21 dake a kan titin Sawmill, unguwar Awa-Ijebu, jihar Ogun kuma dukkan su basu wuce shekaru 19 zuwa 37 ba.

Asali: UGC
KU KARANTA: An kama wani matashi da sassan jikin mutane a Najeriya
Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa wadanda aka kama din maza 23 ne kuma dukkan su daga jami'ar Olabisi Onabanjo dake jihar tare kuma da 'yan matan su su 9 da kuma wasu daga cikin su suka ce dalibai ne a wasu jami'o'in kasar.
Daga karshe kuma hukumar ta EFCC a cikin sanarwar da ta fitar game da batun, ta kuma bayyana cewa da zarar ta kammala bincike akan su to zata kai su kotu domin yi masu hukuncin da ya dace da su.
A wani labarin kuma, Hankula sun tashi a garin Awka, babban birnin jihar Anambra yayin da aka kama wani matashi mai shekaru 19 kacal a duniya mau suna Sunday Owo da ya ziyarci wata asibitin gargajiya da sassan jikin mutane da kuma kwalba cike da jini kulle a cikin buhu.
Kamar yadda muka samu, matashin ya fito ne daga karamar hukumar Ohaukwu ne ta jihar Ebonyi dake makwaftaka da jihar ta Anambra kuma kamar yadda yace, ya zo ne neman maganin yin kudi ko ta halin ka-ka.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng