Duniya-ina-zaki-da mu: An kama wani matashi da sassan jikin mutane da kwalbar jini a Najeriya

Duniya-ina-zaki-da mu: An kama wani matashi da sassan jikin mutane da kwalbar jini a Najeriya

Hankula sun tashi a garin Awka, babban birnin jihar Anambra yayin da aka kama wani matashi mai shekaru 19 kacal a duniya mau suna Sunday Owo da ya ziyarci wata asibitin gargajiya da sassan jikin mutane da kuma kwalba cike da jini kulle a cikin buhu.

Kamar yadda muka samu, matashin ya fito ne daga karamar hukumar Ohaukwu ne ta jihar Ebonyi dake makwaftaka da jihar ta Anambra kuma kamar yadda yace, ya zo ne neman maganin yin kudi ko ta halin ka-ka.

Duniya-ina-zaki-da mu: An kama wani matashi da sassan jikin mutane da kwalbar jini a Najeriya
Duniya-ina-zaki-da mu: An kama wani matashi da sassan jikin mutane da kwalbar jini a Najeriya
Asali: Twitter

KU KARANTA: Rashawa: Ganduje ya kai jaridar da ta tona shi kotu

Legit.ng Hausa ta samu cewa shugabar asibitin gargajiyar ce dai ta tona shi bayan da taga abun tsoron da al'ajabi tare da matashin inda batayi wata-wata ba ta kira 'yan jarida da 'yan sanda domin su shaida hakan.

Tun farko dai matashin, ya bayyana cewa wata mata ce mai suna Blessing -wadda yanzu haka ba'a san inda take ba - ta aike shi ya samo mata sassan jikin tare da yi masa alkawarin samun arziki muddin ya aikata abun da ta umurce shi shikuma bai yi wata-wata ba wajen cika aiki.

A wani labarin kuma, Gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Umar Ganduje ya shigar da jaridar nan ta Daily Nigerian da mawallafin ta, Jaafar Jaafar kara a gaban wata kotun jihar bisa abun da ya kira kazafi da kuma cimasa mutunci da suka yi.

Mai karatu dai zai iya tuna cewa jaridar ta wallafa wasu faya-fayen bidiyoyi ne da suka nuna gwamnan yana karbar cin hanci na miliyoyin kudade daga 'yan kwangila daban daban dake a jihar a watan da ya gabat.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel