Duniya ta zo karshe: Matan Saudiyya na gudanar da zanga-zangar adawa da sa abaya

Duniya ta zo karshe: Matan Saudiyya na gudanar da zanga-zangar adawa da sa abaya

Wasu daga cikin matan Saudiyya sun gudanar da zanga-zangar adawa da tilasta musu sanya abaya, wadda dogowar riga ce da ke rufe tun daga sama har kasa da suke sanyawa a lokacin da za su fita bayyanar jama'a.

Wannan bore dai na gudana ne a shafukan sada zumunta da muhawara, kuma sun sanyawa maudu'in suna ''sanya abaya a bai-bai'', tare da wallafa hotunan mata sanye da abaya da kuma nikabin rufe fuska wadda suke korafin tana takura musu.

Duniya ta zo karshe: Matan Saudiyya na gudanar da zanga-zangar adawa da sa abaya
Duniya ta zo karshe: Matan Saudiyya na gudanar da zanga-zangar adawa da sa abaya
Asali: Getty Images

KU KARANTA: Hukumar DSS ta gayawa Buhari yadda zai yi da Oshiomhole

Legit.ng Hausa ta samu cewa watan Maris da ya wuce, Yarima mai jiran gadon masarautar Saudiyya Muhammad bin Salman bin Abdul'azeez al-Su'ud ya bayyana cewa sanya doguwar abayar ba tilas ba ne ga matan kasar.

Wannan dai na zuwa ne lokacin da mata a Najeriya suke murna Gwamnatin jihar Legas ta amince wa daliban makarantun jihar su saka hijabi a makaranta.

Shugaban kungiyar dalibai musulmai na Najeriya (MSSN) reshen jihar Legas Saheed Ashafa ya sanar da haka.

Ya bayyana cewa gwamnati ta amince da haka ne bisa ga rahotannin tauye hakin dalibai musulman da aka dunga yi a jami’ar Ibadan dake jihar Oyo.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel