Da dumi dumi: Aregbesola ya nada sabon sakataren gwamnatin jihar Osun
- Gwamnan jihar Osun mai barin gado, Mr. Rauf Aregbesola, ya nada sabon sakataren gwamnatin jihar, Dr. Oyebade Ologboyega
- Sanata Mudashiru Hussein, ya sauka daga mukamin SSG, a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin sabon kwamishinan hukumar kidaya ta kasa
- A ranar 27 ga watan Nuwamba, Aregbesola zai mika ragamar mulkin jihar zuwa ga sabon gwamnan jihar, Alhaji Gboyega Oyetola
Gwamnan jihar Osun mai barin gado, Mr. Rauf Aregbesola, ya nada sabon sakataren gwamnatin jihar, Dr. Oyebade Ologboyega. An bayyana wannan nadin na Olowogboyega a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun mai baiwa gwamnan shawara kan watsa labarai, Sola Fasure, a ranar Alhamis.
A ranar Alhami 8 ga watan Nuwamba, tsohon sakataren gwamnatin jihar, Sanata Mudashiru Hussein, ya sauka daga kan wannan mukami nasa, a lokacin da shugaban kasa Muhammadu Buhari ya nada shi a matsayin sabon kwamishinan hukumar kidaya ta kasa a Abuja.
Olowogboyega, wanda kafin wannan sabon nadin nasa, shine shugaban ma'aikata na jihar, a cewar sanarwar, zai ci gaba da rikon mukamin ne a matsayin riko, har zuwa karshen wa'adin gwamnatin Aregbesola.
KARANTA WANNAN: Yaki sai da dabara: Buhari ya kaddamar da wani sabon wayon kamfen

Asali: Twitter
Sanarwar ta ce, "Majalisar zartaswa ta jihar, ta amince da nadin shugaban ma'aikata na jihar, Mr Festus Oyebade Olowogboyega, a matsayin mai rikon kujerar sakataren gwamnatin jihar, zuwa karshen wa'adin wannan gwamnati.
"Ya maye gurbin Sanata Mudashiru Hussain, wanda ya samu karin matsayi zuwa Kwamishinan hukumar NPC ta kasa."
A ranar 27 ga watan Nuwamba, Aregbesola zai mika ragamar mulkin jihar zuwa ga sabon gwamnan jihar, Alhaji Gboyega Oyetola, wanda ya yi dai dai da kwanaki 12 daga ranar da aka nada sabon sakataren gwamnatin jihar.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng