Jiha daya tak ce ke iya biyan mafi karancin albashi na N30,000 bata girgiza ba - Gwamna Yari
Shugaban kungiyar gwamnonin na Najeriya Abdul Aziz Yari dake zaman gwamnan jihar Zamfara yace jihar Legas ce kadan zata iya biyan hakan ita ma don tana samun kudaden shiga da yawa ne ta hanyoyi daban.
Shugaban gwamnonin na Najeriya Abdul Aziz Yari ne ya bayyana hakan jim kadan bayan kammala wani zaman gaggawa da gwamnonin suka gudanar a jiya, garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Asali: Facebook
Tun farko dai Kungiyar gwamnonin Najeriya ta bayyana cewa idan dai har aka dage kan lallai-lallai sai sun biya karin mafi karancin albashi na Naira dubu 30, to fa gaskiya sai dai su rage yawan ma'aikatan su.
KU KARANTA: Manyan birane 10 da suka fi tsadar rayuwa a duniya
Legit.ng Hausa ta samu cewa gwamnan ya kara da cewa Naira dubu 30 tayi masu yawa kuma ba su iya biyan ta domin a lissafin da suka yi ma, jihar Legas ce kadan zata iya biyan hakan ita ma don tana samun kudaden shiga da yawa ne ta hanyoyi daban.
Daga nan ne kuma ya ce tuni kungiyar sa ta nada wani kwamiti na musamman da zai gana da shugaban kasa, Muhammadu Buhari a kan batun domin samun matsaya da kowa zai yi na'am da ita.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng