Jerin sunayen manyan birane 10 da suka fi tsadar rayuwa a duniya a 2018
Wani kwakkwaran bincike da aka gudanar a shekarar nan da muke ciki ta 2018 mai taren "Gano tsadar rayuwa a manyan biranen duniya a shekarar 2018" da wani kamfani mai suna UBS tare da hadin gwuiwar babban bankin duniya ya gano biranen.
Binciken dai mun samu cewa an gudanar da shi ne daga watan Janairu zuwa watan Afrilu na wannan shekarar kuma an tattara alkaluman ne bayan yin nazari kan farashin abinci, kayan masarufi da gidaje dama sauran fannonin rayuwa.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Kwamishinonin Sule Lamido 2 sun sake juya masa baya
Legit.ng Hausa ta samu haka zalika cewa binciken an yi shi ne a biranen duniya akalla 77 inda kuma aka tattara alkaluma daga wurare akalla dubu 75 kuma a ko ina an tattara bayan kayayyaki akalla 128.
Bayan dogon nazari, ga yadda jadawalin biranen suke:
1. Zurich (Switzerland)
2. Geneva (Switzerland)
3. Oslo (Norway)
4. Copenhagen (Denmark)
5. New York (USA)
6. Tokyo (Japan)
7. Milan (Italy)
8. London (United Kingdom)
9. Chicago (USA)
10. Helsinki (Finland)
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng