Ben Nwabueze: Zan rayu har 2019 don ganewa idanuwana nasarar Atiku akan Buhari
- Ben Nwabueze, wani babban lauyan kasar Nigeria (SAN), ya ce zai rayu har zuwa lokacin da Atiku Abubakar, ya doke shugaban kasa mai ci Muhammadu Buhari a zaben 2019
- Nwabueze ya bayyana hakan a ranar Laraba, a lokacin da Atiku Abubakar ya kai masa ziyara ta musamman a gidansa da ke Enugu
- Abubakar ya bayyana wannan haduwar ta sa da Nwabueze a matsayin tuni a garesa kan irin manyan ayyukan kasar da aka gaza kammala aiwatarwa
Ben Nwabueze, wani babban lauyan kasar Nigeria (SAN), ya ce zai rayu har zuwa lokacin da Atiku Abubakar, dan takarar kujerar shugaban kasa karkashin jam'iyyar PDP, ya doke shugaban kasa mai ci Muhammadu Buhari a zaben 2019, don zama sabon angon kasar.
Nwabueze ya bayyana hakan a ranar Laraba, a lokacin da Atiku Abubakar ya kai masa ziyara ta musamman a gidansa da ke Enugu.

Asali: Twitter
Segun Showunmi, mai magana da yawun kungiyar yakin zaben Atiku Abubakar, ya wallafa hotunan manyan kasar guda biyu a lokacin da suka rungume juna cikin shaukin sake haduwa.
KARANTA WANNAN: Iyaye, dalibai, masu ruwa da tsaki sun fara kokawa kan dadewar yajin aikn ASUU
Haka zalika shima Atiku ya wallafa wadannan hotunan nasa tare da babban lauyan mai shekaru 86 a kan shafinsa na Twitter.

Asali: Twitter
Abubakar ya bayyana wannan haduwar ta sa da Nwabueze a matsayin haduwa mai sanya karsashi, yana mai cewa babban lauyan ya tuna masa irin "manyan ayyukan kasar da aka gaza kammala aiwatarwa."
"Farfesa Ben Nwabueze dan kasa ne na-gari kuma daya daga cikin manyan lauyoyin kasar. A wata ganawa ta musamman da shi a Enugu, har ya yi mun tuni kan irin manyan ayyukan kasar da aka gaza kammala aiwatarwa. Ina mai bashi tabbaci da ma daukacin yan Nigeria cewa, zan cika dukkanin alkawuran dana dauka," a cewar Atiku, kamar yadda ya wallafa a shafinsa na Twitter.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng