Da dumin sa: Rundunar sojin ruwan Najeriya sun kaddamar da yakin sunkuru kan barayin mai

Da dumin sa: Rundunar sojin ruwan Najeriya sun kaddamar da yakin sunkuru kan barayin mai

Rundunar sojojin ruwan Najeriya shiyyar Gabashin kasar nan sun sanar da kaddamar da wani gagarumin yakin sunkuru akan barayin mai da kuma tsagerun Neja Delta da nufin kakkabe dukkan bata garin yanki.

Rundunar dai ta bayyana cewa ta dauri damarar kaddamar da yaki da bata garin nan ta hanyar wani atisaye da suka soma mai suna “Ani-Oforifori’’ da yarin Kalabari da ke nufin 'A-kori-barayi' da Hausa.

Da dumin sa: Rundunar sojin ruwan Najeriya sun kaddamar da yakin sunkuru kan barayin mai
Da dumin sa: Rundunar sojin ruwan Najeriya sun kaddamar da yakin sunkuru kan barayin mai
Asali: Facebook

KU KARANTA: Karin Albashi: An ba Buhari dama ta karshe

Legit.ng Hausa ta samu cewa wannan dai na kunshe ne a cikin wata sanarwa da jami'in hulda da jama'a na rundunar ta sojin ruwa inda a ciki kuma suka tabbatar da cewa ba sani-ba-sabo.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake bada agajin gaugawa da rage radadin bala'I watau National Emergency Management Agency, (NEMA) ta bayyana cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun tafka gagarumar sata a kauyen karamar hukumar Jere, jihar Borno.

Malam Bashir Garga, dake zaman jami'an hukumar dake kula da shiyyar Arewa maso gabashin kasar shine ya bayyana hakan inda yace 'yan ta'addan sun sace shanu 200, tumakai 300 da awakai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng