Halin dan Akuya: ICPC za ta gurfanar da Farfesan da jami'ar OAU ta kora daga aiki

Halin dan Akuya: ICPC za ta gurfanar da Farfesan da jami'ar OAU ta kora daga aiki

Hukumar yaki da cin hanci da almundahana (ICPC) ta kammala shirin gurfanar da Farfesa Richard Akindele da jami'ar Obafemi Awolowo (OAU) ta kora daga aiki bayan samun sa da nuna halin dan akuya a kan wata daliba.

ICPC za ta gurfanar da Farfesa Akindele ne a gaban kotun gwamnatin tarayya da ke Osogbo a jihar Osun.

Halin dan Akuya: ICPC za ta gurfanar da Farfesan da jami'ar OAU ta kora daga aiki
Halin dan Akuya: ICPC za ta gurfanar da Farfesan da jami'ar OAU ta kora daga aiki
Asali: Twitter

DUBA WANNAN: Masifar da ta fi Boko Haram na nan tafe a kasar nan - Sarki Sanusi

Farfesa Akindele ya shiga bakin duniya ne bayan wata dalibar sa, Monica Osagie, ta kwarmata wata hira da su ka yi a waya, inda ya ke neman ta bashi hadin kai ya yi lalata da ita matukar tana bukatar cin jarrabawar darasin da ya koyar da su.

Za a gurfanar da Farfesa Akindele ne a ranar 19 ga watan Nuwamba bisa tuhumar sa da laifin amfani da matsayinsa na malamin jami'a domin neman yin lalata da daliba da kuma saba ka'ida da cin amanar aiki.

Sai dai Farfesa Akindele ya nemi a sirrinta sauraron karar ta sa bayan ya amsa laifinsa. Kazalika ya bayyana cewar ba shi da koshin lafiyar da zai iya zama a gidan.

Da ya ke mika wannan bukata ga hukumar ICPC ta bakin lauyansa, Farfesa Akindele, ya ce a shirye ya ke ya yi biyayya da duk hukuncin da kotu ta yanke a kansa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: : https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng