Babbar magana: Kotu ta kori wani dan majalisa don ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

Babbar magana: Kotu ta kori wani dan majalisa don ya sauya sheka daga PDP zuwa APC

- Wata babbar kotun da ke Uyo, a ranar Laraba, ta ayyana kujerar dan majalisa a jihar Akwa Ibom a matsayin wofi, bayan sauya sheka daga PDP zuwa APC

- Dan majalisar wanda lamarin ya shafa, Idongesit Ituen, na wakiltar mazabar Itu State, a majalisar dokoki ta jihar Akwa Ibom

- Sai dai lauyan Mr Ituen, Uyo-Obong Jumbo, ya bayyana cewa za su daukaka kara kan wannan hukuncin da babbar kotun gwamnatin tarayyar ta yanke

Wata babbar kotun gwamnatin tarayya da ke Uyo, a ranar Laraba, ta ayyana kujerar wani dan majalisa a jihar Akwa Ibom a matsayin wofi, wanda ya sauya sheka daga jam'iyyar PDP zuwa jam'iyya mai mulki ta APC.

Dan majalisar wanda lamarin ya shafa, Idongesit Ituen, na wakiltar mazabar Itu State, a majalisar dokoki ta jihar Akwa Ibom.

Mr Itue ne ya shigar da wannan kara a watan Satumba na wannan shekarar, inda ya bukaci kotun da ta dakatar da kakakin majalisar dokoki na jihar, Onofiok Luke, daga ayyana kuerarsa a matsayin wofi.

KARANTA WANNAN: CNN ta maka Trump kotu kan dakatar da wani babban jami'inta daga shiga White House

Babbar magana: Kotu ta kori wani dan majalisa don ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Babbar magana: Kotu ta kori wani dan majalisa don ya sauya sheka daga PDP zuwa APC
Asali: Depositphotos

Banda kakakin majalisar, sauran wadanda aka shigar da su karar sun hada da jam'iyyar PDP, hukumar zabe mai zaman kanta ta kasa INEC, da kuma kwamishinan 'yan sanda na jihar Akwa Ibom.

Mr Luke, ya shigar da karar martani, inda ya bukaci kotun da ta "ayyana hakan, la'akari da cewa ya sauya sheka daga PDP zuwa APC kafin karewar wa'adin mulkinsa na shekaru hudu kamar yadda aka zabe shi, Hon. Idongesit Ntuen ya rasa kujerarsa a majalisar dokoki ta jihar Akwa Ibom.

KARANTA WANNAN: Da dumi dumi: Gwamnoni sun kira taron gaggawa kan karin albashi mafi karanci

"Don haka muke bukatar kotu da ta ayyana kujerar Hon Idongesit Ituen a matsayin wofi tare da korarsa daga majalisar dokoki ta jihar cikin gaggawa."

Kotun wacce ke karkashin jagoranci mai shari'a F. O. Riman, ta kori karar da Mr Ituen ya shigar, tare da amincewa da karar da Mr. Luke ya shigar, na korar dan majalisar daga kujerarsa.

Sai dai lauyan Mr Ituen, Uyo-Obong Jumbo, ya shaidawa jaridar PREMIUM TIMES a ranar Laraba cewa za su daukaka kara kan wannan hukuncin da babbar kotun gwamnatin tarayyar ta yanke.

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng