Ganduje ya yi namijin kokari a jihar Kano – Shugaba Buhari

Ganduje ya yi namijin kokari a jihar Kano – Shugaba Buhari

Shugaba Muhammadu Buhari ya siffanta gwamnan jihar Kano, Dakta Abdullahi Ganduje, a matsayin shugaba na kwarai kuma ya yabawa irin namijin kokarin da yakeyi a jihar Kano.

Shugaban kasan ya bayyana hakan ne a wani hira da yayi yan Najeriya a birnin Faris, kasar Faransa.

Buhari ya yabawa aikin da Ganduje yayi a bangaren ilimi da kiwon lafiya inda yace:

“Na yabawa gwamnan da yin ayyuka da dama. Ya taba gayyata na kuma naje Kano. Ayyukan da Kwankwaso ya fara a bangaren ilimi da kiwon lafiya, Ganduje ya kammalasu.”

“Ya kammalasu kuma mutanen jihar Kano na jin dadinsu yanzu. Gaskiya mutumin kirki ne,”

KU KARANTA: Da duminsa: Ganduje ya gabatar da kasafin kudin 2019 na N219bn

Mun kawo muku rahoton shugaba Muhammadu Buhari ya yi magana kan zargin da ake yiwa gwamnan jihar Kano, Abdullahi Umar Ganduje, inda yace za'a dau mataki kan al'amarin.

Jaridar Daily Nigerian ta bada rahoton cewa Shugaba Buhari ya yi wannan magana ne yayinda wani dalibi dan asalin jihar Kano a kasar Faransa yabi irin ayyukan da gwamnan keyi kuma yayi kira ga gwamnatin tarayya ta bi sahunsa.

Kan ya gama magana, shugaba Buhari ya tambayi dalibin shin ya ga bidiyon da aka nuna gwamnan yana karban daloli?

Yace: "A bangare guda, shin baka ga bidiyoyin gwamnan inda yake cusa daloli cikin garensa ba?"

"Mun baiwa hukumomin tsaro bidiyoyin domin bincike. Kuma za mu dau mataki akan abin inda aka same shi da kashi a gindi."

Sanarwa: Shafin Naij.com Hausa shine yanzu ya koma Legit.ng Hausa, don inganta muku zafafan labarai dama kayatarwa

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/hausa.legit.ng

Twitter: https://twitter.com/hausa.legit.ng

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng