Harka ta lalace: Maciji ya makalewa wani mai wasa da shi a cikin baki a Najeriya (Bidiyo)

Harka ta lalace: Maciji ya makalewa wani mai wasa da shi a cikin baki a Najeriya (Bidiyo)

Daman dai Hausawa na cewa dukkan mai wasa da maciji to idan ba sa'a ba shine zai yi silar ajalin sa. Wasa da maciji dai ya zama tamkar ruwan dare a kasar Najeriya inda wasu kan dauki hakan tamkar sana'a da sukan yi domin su samu taro da sisi.

Za'a iya ganin irin mutanen nan a kasuwanni, bakin hanya ko kuma inda mutane kan taru suna wasa da macijin domin kayatar da masu tafiya ko kuma masu sha'awa da kan zo kallon su har ma kuma su basu wani abu.

Harka ta lalace: Maciji ya makalewa wani mai wasa da shi a cikin baki a Najeriya (Bidiyo)
Harka ta lalace: Maciji ya makalewa wani mai wasa da shi a cikin baki a Najeriya (Bidiyo)
Asali: Facebook

KU KARANTA: Hanya 6 na kare kai daga cutar suga

Wasu kuma musamman ma masu saida magani irin na gargajiya kan yi anfani da macijin domin jan hankalin al'uma.

Legit.ng Hausa ta ci karo da wani faifan bidiyo na wani mai wasa da maciji a birnin Legas, tarayyar Najeriya da yake ta kokowa da wani macijin da ya saka a cikin bakin sa yana wasa da shi amma kuma yaki fitowa.

Mun dai ga bidiyon inda mutumin yake sanye da bakaken kaya yana ta kuma kokarin amayo da macijin daga cikin bakin sa amma ya ki amayuwa.

Ga dai bidiyon nan:

To wannan dai kam sai dai muce Allah ya kiyaye!

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng