A cikin shekara 1: An samu rahoton cikin shege 1,371,000 a Nigeria

A cikin shekara 1: An samu rahoton cikin shege 1,371,000 a Nigeria

An samu rahotonni da ke nuna cewa, a cikin shekarar 2018 kacal, an samu cikin shege 1,374,000 (sama da miliyan daya da dari ukku), kamar dai yadda hukumar tsarin kayyade haihuwar iyalai ta duniya ta wallafa wannan rahoto.

A cewar rahoton, a cikin wannan shekarar da muke ciki ta 2018, an zubar da ciki ba bisa ka'ida ba, wanda zai iya jawowa matan matsala, akalla sau 735,000 (sama da dubu dari bakwai).

Jaridar The Cable ce ta samu wannan rahoto, kuma aka bayyana ci a babban taro na kasa da kasa da ke kan gudana a Kigali, babban birnin kasar Rwanda, kan tsarin kayyade haihuwar iyali.

KARANTA WANNAN: Jam'iyyarka ta PDP ba zata iya daukar nauyin yakin zabenka ba - APC ta yiwa Atiku shagube

A cikin shekara 1: An samu rahoton cikin shege 1,371,000 a Nigeria
A cikin shekara 1: An samu rahoton cikin shege 1,371,000 a Nigeria
Asali: UGC

Rahoton ya ci gaba da bayyana cewa, sama da kashi 13.8 na matan Nigeria, na amfani da kwayoyin zubar da ciki a 2018.

Rahoton ya bayyana cikin shege a matsayin "Adadin lokacin da ake samun shigar ciki a jikin mace, a lokacin da ita macen ko shi namijinm ko kuma gaba dayansu, basu shirya zuwan cikin ba, ko karin haihuwa, ko kuma suna son bayar da tazarar haihuwa."

"Ana auna wannan ne ta hanyar la'akari da cikin da aka dauka na baya, da kuma nazari kan cikin da aka dauka yanzu," a cewar rahoton.

A hannu daya kuwa, masana kimiyya daga jami'ar koyon kiwon lafiyar al'umma ta Havard, ta kirkiro wani sinadari na musamman, da mata za su yi amfani da shi don daukar ciki a gaggawa.

Cikakken bayani kan hakan na zuwa...

SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng