Ziyarar ba-zata: Abubuwa 4 da Kwankwaso yayi da yaje jihar Kano

Ziyarar ba-zata: Abubuwa 4 da Kwankwaso yayi da yaje jihar Kano

Yanzu haka dai, jagoran darikar siyasa ta Kwankwasiya kuma tsohon gwamnan Kano, kuma mai wakiltar mazabar Kano Tsakiya a majalisar dattijan Najeriya, Sanata Rabi'u Musa Kwankwaso ya shiga jihar ta Kano, kuma kawo yanzu ma yana can.

Makusantan tsohon gwamnan haka zalika sun bayyana cewa Sanatan na gudanar da wata ziyara ta kwanaki irinta ta farko a jihar tun da ya bar kujerar gwamnan Kano a shekarar 2015.

Sanata Kwankwaso ya ziyarci birnin na Kano ne ba tare da sanar da cewa zai kai ziyarar ba, abin da ya zo wa magoya bayansa da dama ba zata.

Ziyarar ba-zata: Abubuwa 4 da Kwankwaso yayi da yaje jihar Kano
Ziyarar ba-zata: Abubuwa 4 da Kwankwaso yayi da yaje jihar Kano
Asali: Facebook

KU KARANTA: An gano samfurin wake mai guba a kasuwannin arewacin Najeriya

Legit.ng ta tattaro maku wasu muhimman abubuwan da Sanatan yayi yayin ziyarar tasa kawo yanzu:

1. Gaisawa da masoyansa da abokan arziki:

Babban abin da ziyarar ta sanata Rabi'u Musa Kwankwaso a Kano ita ce ganawa da masoyansa da abokan arziki, musamman wadanda ba su taba ganinsa ba tun bayan barinsa mulkin Kano.

2. Ta'aziyya:

Sanata Kwankwaso ya ce ya kuma yi amfani da lokacin ziyarar a Kano domin yin ta'aziyyar wasu da rashe-rashe da aka yi a Kano, wanda bai samu damar zuwa ta'aziyya ba.

3. Ya zauna da 'yan takara:

Daya daga cikin muhimman abubuwan da Kwankwason ya yi a yayin ziyarar ta sa jihar da ya yi wa gwamna sau biyu, ita ce, ganawa da 'yan takara na jam'iyyar PDP.

4. Ziyarar Sarkin Kano:

A yayin ziyar da Kwankwaso ya kai Kano, ya kai wa Sarkin Kano Malam Muhammadu Sanusi na biyu ziyara a fadarsa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng