Buhari yayi wani muhimmin roko ga kasashen waje game da barayin gwamnati

Buhari yayi wani muhimmin roko ga kasashen waje game da barayin gwamnati

Shugaban kasar Najeriya, Muhammadu Buhari ya bukaci kasashen duniya da 'yan Najeriya suka saci kudin gwamnati suka je suka killace da su taimaka su maido masa kudin domin gwamnatin sa ta samu kudaden yin ayyukan cigaba.

Shugaba Buhari, wanda ya je birnin Paris na kasar Faransa don halartar wani muhimmin taro don tunawa tabbatar da kawo karshen yakin duniya na daya, ya gaya ma al’ummar Najeriya mazauna kasar Faransa cewa gwamnatin sa ba ta da kudin yin ayyukan da take so don wasu 'yan tsiraru sun sace.

Buhari yayi wani muhimmin roko ga kasashen waje game da barayin gwamnati
Buhari yayi wani muhimmin roko ga kasashen waje game da barayin gwamnati
Asali: Facebook

KU KARANTA: Shekarau yayi magana game da cire sunan sa a cikin 'yan takara

Legit.ng Hausa ta samu cewa Shugaban kasar ya kuma kara da cewa da dan bin da kasar ke da shi a halin yanzu da bai taka-kara-ya-karya ba ne ya ke lallabawa alhalin kuwa ga dinbin dukiyar Najeriya wasu mutane ‘yan kalilan sun boye a kasashen waje.

Haka ma dai a wata takardar bayani, wadda Mai Bai Wa Shugaban Kasa Shawara kan harkokin jarida Femi Adesina ya rattaba wa hannu, Shugaba Buhari ya tabbatar ma ‘yan Najeriya din cewa duk da wannan matsala ta rashin kudi, gwamnatin Najeriya za ta cigaba da mai da hankali kan bangaren ilimi, hanyoyi, lantarki, da kuma sauran ayyuka na gina kasa.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Online view pixel