Jami'an kwastam sun kama manyan bindigu da aka shigo da su Najeriya
- Jami'an kwastam sun kama manyan makamai da aka shigo da su Najeriya ta barauniyar hanya
- Sun kuma kama kayan sojoji 200, buhuhunan shinkafa 430 wanda farashin sa ya kai naira miliyan tara, kwalaben kodin 1, 160 da kuma tramadol sinki 300
- Rundunar kwasta din ta sanar da kama mutane uku da aka kama da kayayyakin sannan kuma ta ce za'a gurfanar da su
Hukumar kwastam na Najeriya reshen Zone C, a ranar Talata, 13 gawatan Nuwamba sun sanar da kama manyan bindigogi , alburusai da kuma kayan sojoji 200.
Sun kuma bayyana cewa sun kama buhuhunan shinkafa 430 wanda farashin sa ya kai naira miliyan tara, kwalaben kodin 1, 160 da kuma tramadol sinki 300.

Asali: Facebook
Yayinda ake nuna kayayyakin da suka kama, kwanturolan reshen, Mista Kayode Olusemire, ya bayyana ewa an kama mutane uku sannan kuma za’a gurfanar da su.
Olusemire yace an kama miyagun kwayoyin a Onitsha, Anambra yayinda aka kama makaman a Enugu.
KU KARANTA KUMA: APC ta sake rasa wasu mambobinta inda suka koma PDP
Ya kuma bayyana cewa an kama shinkafar ne a hanyar Port Harcourt-Aba.
Daga karshe ya yi watsi da ayyukan masu fasa kwauri inda ya bukaci jama’a da su basu hadin ai wajen yaki da hakan.
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta LEGIT NG Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng