Gwamnatina za ta magance matsaloli 7 da Nigeria ke fuskanta - Ezekwesili
Dr. Obiageli Ezekwesili, yar takarar shugaban kasar Nigeria karkashin jam'iyyar Allied Congress Party of Nigeria (ACPN), ta bayyana cewa ta gano wasu matsaloli guda 7 da ke ciwa Nigeria tuwo a kwarya, haka zalika ta gano hanyoyin magance wadannan matsalolin, ma damar dai yan kasar za su bata dama a zaben 2019.
Bayanin hakan na daga cikin bayanan da ta gabatar kan tsare tsaren gwamnatinta idan ta hau mulki, wanda ta karantasu ga manema labarai a ranar Litinin, a Legas.
Ezekwesili wacce ta taba rike mukamin ministar ilimi da kuma albarkatun kasa, ta kuma jaddada kiranta ga 'yan Nigeria na su ki zabar APC ko PDP a babban zabe na 2019.
KARANTA WANNAN: Buhari ya ce kudaden Nigeria da aka sace an boye su a Amurka da kasashen Turai

Asali: UGC
Oby Ezekwesili ta ce, "akwai wasu matsaloli guda bakwai da suka dade suna ciwa kasar tuwo a kwarya. Domin magance wadannan matsalolin, dole ayi aiki tukuru, dole a samar da shugabanci mai kunshe da karfafan manufofi da ta sanya kasar a gabanta."
Matsalolin da Dr. Obiageli Ezekwesili ta lissafa sun hada da:
1. Karancin ayyukan farfado da tattalin arzikin kasar da ya durkuse: Kamar dai ace babbar kasar irin Nigeria, kiyascin kudin tattalin arzikin kasar da ya kai $375.77bn bayan shekaru 58 da samun 'yanci ya shiga cikin mawuyacin hali. Farfado da wannan tattalin arziki da dawo da martabarsa a idanun duniya shine burin gwamnatin ACPN.
2. Tsantsar talauci da nuna wariya: A har kullum talauci kara karuwa yake a Nigeri da akalla mutane 6 a kowanne minti daya. Zuwa lokacin da zan kammala wannan jawabin nawa, akalla yan Nigeria 250 ne za su shiga cikin matsanancin talauci. A cewar rahoton talauci na duniya, idan har kasar taci gaba da tafiya a haka, to kuwa adadin yan nawa da zasu afka cikin kangin talauci zai tashi daga 88m zuwa 120mm a 2030. Nuna tsantsar wariya tsakanin talaka da mai kudi, na daga manyan kalubalen da suka tilasta karuwar masu shiga cikin kuncin talauci a kasar.
3. Tabarbarewar tsaro da karuwar rikice-rikice: Nigeria a yau, itace kasa ta 14 daga cikin kasashen duniya da ke fama da rikice rikice, ta 16 da ke da hatsarin rayuwa a ciki, a cewar wani rahoto na zaman lafiya na duniya. Kasar na fuskantar nau'o'in rikice rikice guda 14 a shiyyoyi daban daban, kama daga ta'addanci, rikicin makiyaya da manoma, garkuwa da mutane, safarar mutane da dai sauransu. Zaka tura yaranka mata makaranta da safe don neman ilimi, amma zuwa rana an kawo maka labarin cewa na sace su. An jefa al'ummomi da dama cikin fargaba da yunwa da talauci.
4. Tsantsar jalilci: Akalla kananan yara 13.5m ne suka fita daga makaranta sakamakon dalilai da dama. Adadin yawan nasu ya zarce adadin yawan jama'ar kasar Benin. Ko wadanda ke da damar zuwa makaranta a wannan zamani na samun ilimi maras inganci. Ilimi shi ne kudiri na farko a gwamnatina. Zan tabbata na cire duhun jahilci a kasar idan har aka bani dama na zama shugabar kasa.
5. Matsalolin kiwon lafiya da walwalar jama'a: Hukumar lafiya ta kasa (WHO) ta bayyana Nigeria a matsayin kasa ta 187 cikin 190 a fannin kiwon lafiya. A wajen bunkasa walwalar jama'a kuwa, Nigeria ce ta taran karshe cikin kasashe 157. Na sha alwashin baiwa fannin lafiya fifici a gwamnatina. Nigeria na rasa abubuwa da yawa idan har jama'artanna fama da matsalolin kiwon lafiya.
6. Rashin ababen more rayuwa: Kasarmu ta zamo koma baya wajen ayyukan more rayuwa, da suka hada da tituna rashin wutar lantarki, rashin hanyoyin sadarwa, rashin tasoshin jiragen ruwa da na layin dogo. Akwai baraka babba a bunkasar tattalin arzikin kasar sakamakon rashin ababen more rayuwa. Shin idan baka bunkasa rayuwar jama'a ba, ta ya ya za a samu ci gaba?
7. Rashin ingantaccen tsarin gudanarwar gwamnati: Tsarin da gwamnati ke amfani da shi na tafiyar da ayyukanta sam basu bisa hanyar dai-dai. Tsari mai kyau shi ke samar da tallafi, da kuma kyakkyawar manufa ga gwamnatin tarayya. A zabe 2015, gwamnatin APC ta yi alkawarin sake fasalin kasar, amma da ta hau sai ta yi watsi da wannan alkawari. Amma ni, ina mai tabbatar maku, zan samar da kyakkyawan tsarin shugabanci, da zai kawo kyakkyawan ci gaba ga kasar.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng