Mambobin PDP 900 sun sauya sheka zuwa APC a Jigawa

Mambobin PDP 900 sun sauya sheka zuwa APC a Jigawa

Akalla mambobin jam’iyyar Peoples Democratic Party (PDP) 900 ne suka sauya sheka zuwa jam’iyyar All Progressives Congress (APC) a karamar hukumar Kaugama, da ke jihar Jigawa a ranar Litinin, 12 ga watan Nuwamba.

Da yake tarban masu sauya shekar a Kaugama, mataimakin gwamnan jihar, Alhaji Ibrahim Hassan ya bukace su da su yi aiki don ganin nasarar jam’iyyar a zaben 2019.

“Sauya shekar ku zuwa APC ya nuna cewa jam’iyyar ta sake karfi sosai yayinda muke tunarar zaben 2019,” inji shi.

Mambobin PDP 900 sun sauya sheka zuwa APC a Jigawa
Mambobin PDP 900 sun sauya sheka zuwa APC a Jigawa
Asali: Depositphotos

Shugaban APC, Alhaji Yusuf Ubale ya yaba ma masu sauya shekar kan shawarar da suka yanke, cewa kofar jam’iyyar a bude ta ke ga duk wanda ke son sauya sheka.

KU KARANTA KUMA: 2019: Dan takarar kujeran dan majalisa na APC a Adamawa ya koma PDP

“Za mu yi adalci ga duk wanda ya shigo APC ko yake da ra’ayin shiga jam’iyyar,” inji shi.

Daga nan sai Ubale ya ba mambobin jam’iyyar da suka fadi zaben fidda gwani hakuri, inda ya basu tabbaci cewa jam’iyyar za ta karramasu kan biyayyar da suka yi.

Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa

Ko a http://twitter.com/legitnghausa

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa

Asali: Legit.ng

Online view pixel