2019: Dan kashenin Buhari tare da mazauna Kano sun yi addu’o’i da sallah na musamman ga Buhari
Wani mamba na majalisar wakilai daga jihar Kano, Honourable Abdulmumin Jibril ya bi sahun sauran mazauna Kano wajen gudanar da addu’o’i da sallah na musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari.
A wani rubutu dan majalisan ya wallafa a shafin twitter a ranar Litinin, 12 ga watan Nuwamba ya ce an gudanar da addu’an ne a ranar Lahadi, 11 ga watan Nuwamba.
Dan majalisan ya ce an kuma gudanarwa da Gwamna Umaru Ganduje na jihar Kano ma addu’an.
Ya rubuta: “Addu’o’i na musamman ga Shugaban Kasa Muhammadu Buhari, Gwamna Kanduje, Najeriya, Kano da kuma yankin Kiru/Bebeji. Mallam Ahmad Sulaiman Ibrahim ne ya jagoranci karatun Qur’ani da muryarsa."
KU KARANTA KUMA: Magu ya yi buris da tambaya akan bidiyon cin hanci na Ganduje
Idan ka na da wata shawara ko bukatar ba mu labari, a tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng
Ku same mu a https://www.facebook.com/legitnghausa
Ko a http://twitter.com/legitnghausa
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Shafin NAIJ Hausa ya koma Legit.ng Hausa
Asali: Legit.ng