Hukumar EFCC ta kammala bincike kan Babachir Lawal, ta tabbatar da zargin da ake masa kuma zai gurfana a kotu

Hukumar EFCC ta kammala bincike kan Babachir Lawal, ta tabbatar da zargin da ake masa kuma zai gurfana a kotu

Hukumar hana almundahana da yiwa tattalin arzikin kasa zagon kasa wato EFCC ta kammala bincikenta kan zargin almundahana da babakere da akayiwa tsohon sakataren gwamnatin tarayya, Babachir David Lawal.

Yayinda yake kujeran sakatare, ana tuhumar Babachir Lawal da laifin satan kudin shirin fadar shugaban kasa na taimakawa jama’an yankin arewa maso gabas. Amma har yanzu bai gushe yana musanta hakan ba.

KA KARANTA: An damke Sanata Hope Uzodinma da laifin cinye kudin kwangila

Binciken da shugaban hukumar EFCC, Ibrahim Magu, ya aikawa babban lauyan tarayya kuma ministan Shari’a, Abubakar Malami, na nuna cewa lallai yana da kasha a gindi. Majiyoyi daban-daban sun tabbatar da cewa lallai Magu ya kawowa Malami takardan a makon jiya.

Hukumar EFCC ta kammala bincike kan Babachir Lawal, ta tabbatar da zargin da ake masa kuma zai gurfana a kotu
Hukumar EFCC ta kammala bincike kan Babachir Lawal, ta tabbatar da zargin da ake masa kuma zai gurfana a kotu
Asali: Depositphotos

Takardan kammala binciken ya hada da irin matakan da za’a dauka kan tsohon na kusa da shugaba Buhari kuma ya gurfana a gaban kotu.

A ranan 30 ga watan Oktoba 2017, shugaba Muhammadu Buhari ya karbi takardan kwamitin shawarwari da bincike wanda mataimakin shugaban kasa, Yemi Osinbajo, ya jagoranta domin gano gaskiyan zargin da akeyiwa Babachir Lawal, da tsohon shugaban NIA, Ayodele Oke.

Daga baya shugaba Buhari ya salami Babachir Lawal daga kujeran sakatare.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng