Atiku ba barawo bane, ba zai taba satar dukiyar Najeriya ba, a cewar matar sa Titi

Atiku ba barawo bane, ba zai taba satar dukiyar Najeriya ba, a cewar matar sa Titi

Titi Abubakar, matar dan takarar shugaban kasa a karkashin jam'iyyar PDP, Atiku Abubakar, ta ce mijinta ba barawo ba ne kuma ba zai taba satar dukiyar Najeriya ba.

Titi ta bayyana haka ne yayin da wata kungiyar mata ta kai ma ta ziyara a gidanta da ke Abuja.

Ta bayyana cewar Atiku attajiri ne da ba zai taba shiga takarar neman shugabancin Najeriya don kawai ya yi sata ba.

"Ya shiga takara ne kawai don bawa Najeriya gudunmawa kamar yadda shi ma kasar ta bashi gudunmawa wajen zama abinda ya zama.

"Atiku ya rasa mahaifinsa tun yana karami, ya tashi ne a hannun mahaifiyar sa, wacce ya fara yiwa talla domin samun kudin daukan nauyin karatun sa.

Atiku ba barawo bane, ba zai taba satar dukiyar Najeriya ba, a cewar matar sa Titi
Titi Abubakar da kungiyar mata
Asali: Facebook

"Saboda irin kalubalen da ya fiskanta na tashi a hannun mace, Atiku ya kasance mai matukar tausayi da jin kai ga mata da matasa.

"Hakan ne ma ya sa shi daukan alkawarin cewar zai bawa mata da matasa kashi 40% na makaman gwamnati, idan aka zabe shi a matsayin shugaban kasa," a cewar Titi.

DUBA WANNAN: Buhari ya ci abinci tare da shugabannnin duniya a kasar Faransa, Hotuna

Titi ta kara da cewar ana bata sunan Atiku ne kawai ta hanyar cewa ya yi sata saboda wasu mutane ba sa son ya zama shugaban kasa.

Ta kara da cewa har yanzu babu wata hukumar yaki da cin hanci da ta taba gayyatar Atiku domin bincikensa a kan cin hanci.

A nata bangaren, shugabar kungiyar matan, Princess Ngozi, ta ce sun roki Allah domin ya bawa Atiku nasara a zabe mai zuwa domin ceto Najeriya daga mawuyacin halin da tsinci kanta.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma LEGIT.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=ng.legit.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://facebook.com/legitnghausa

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.ng

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng