Rundunar sojojin Najeriya sun yi wa shekau mummunar barna a dajin Sambisa

Rundunar sojojin Najeriya sun yi wa shekau mummunar barna a dajin Sambisa

Rundunar sojin Najeriya da yanzu haka take yakarr 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, ta yi ikirarin cewa dakarunta sun kashe kwamandojin kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter da safiyar ranar Lahadi ta kara da cewa dakarunta sun kwace wasu kauyuka daga hannun mayakan kungiyar.

Rundunar sojojin Najeriya sun yi wa shekau mummunar barna a dajin Sambisa
Rundunar sojojin Najeriya sun yi wa shekau mummunar barna a dajin Sambisa
Asali: UGC

KU KARANTA: Hotunan yadda Kanawa suka tarbi Kwankwaso da yaje gida

Legit.ng Hausa ta samu cewa wadanda jam'an sojojin suka kashe kamar yadda suka bayyana sune Abu Rajal da Tuja Sa'inna Banki lokacin da ake kakkabe yankunan Gumsuri da Gambori daga 'yan Boko Haram.

A baya dai babban hafsan rundunar sojin kasa Laftanar Janar TY Buratai ya yaba wa dakarun da suka yi wannan aiki sannan ya bukace su da su ci gaba da kakkabe ragowar mayakan Boko Haram.

A wani labarin kuma, Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake bada agajin gaugawa da rage radadin bala'I watau National Emergency Management Agency, (NEMA) ta bayyana cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun tafka gagarumar sata a kauyen karamar hukumar Jere, jihar Borno.

Malam Bashir Garga, dake zaman jami'an hukumar dake kula da shiyyar Arewa maso gabashin kasar shine ya bayyana hakan inda yace 'yan ta'addan sun sace shanu 200, tumakai 300 da awakai.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng