Allah ya tsine: An hana musulmai yin sallah sau 5 a kasar Indiya
- An hana musulmai yin sallah sau 5 a kasar Indiya
- Yanzu sallar juma'a kawai suke yi a masallacin
- Yan garin sun nuna matukar fushin su ga gwamnati
Labarin da muke samu daga majiyoyin mu da dama na nuni ne da cewa mahukunta a kasar Indiya a wani gari da ake kira Taj Mahal sun hana musulman su aiwatar da sallolin su a masallacin unguwar mai daddaden tarihi.

Asali: Depositphotos
KU KARANTA: Ku karanta firar Rahama Sadau da masoyin ta a Tuwita
Da yake bayyana hakan ga manema labarai na yankin a cikin fushi, daya daga cikin masallatan masallacin kuma limamin su, Syed Sadiq Ali ya ce mahukuntan sun hana su salloli biyar a masallacin kuma ba tare da wata kwakkwarar hujja ba.
Legit.ng Hausa ta samu cewa tun farko dai kotun koli ta kasar Indiya din ce a watan Yulin da ya gabata ta yanke hukuncin hana wadanda ba musulmai ba yin ibadun su a masallacin garin.
Sai dai kuma musulmai sun ce yanzu hadda su aka hana gudanar da ibadojin su a masallacin sai dai sallar Juma'a kawai ake barin su suyi.
Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.
Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,
Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng