Wuya makarantar kare: 'Yan Boko Haram sun koma satar dabbobi

Wuya makarantar kare: 'Yan Boko Haram sun koma satar dabbobi

Hukumar nan ta gwamnatin tarayya dake bada agajin gaugawa da rage radadin bala'I watau National Emergency Management Agency, (NEMA) ta bayyana cewa 'yan ta'addan Boko Haram sun tafka gagarumar sata a kauyen karamar hukumar Jere, jihar Borno.

Malam Bashir Garga, dake zaman jami'an hukumar dake kula da shiyyar Arewa maso gabashin kasar shine ya bayyana hakan inda yace 'yan ta'addan sun sace shanu 200, tumakai 300 da awakai.

Wuya makarantar kare: 'Yan Boko Haram sun koma satar dabbobi
Wuya makarantar kare: 'Yan Boko Haram sun koma satar dabbobi
Asali: UGC

KU KARANTA: Peter Obi yayiwa Gwamna El-rufa'i kashedi

Legit.ng Hausa ta samu cewa Malam Garba a cikin wata sanarwa dauke da sa hannun sa, ya ce 'yan ta'addan dauke da muggan makamai sun dira a kauyen na Bale-Shuwa na karamar hukumar Jere da dare inda kuma sukayi awon gaba da dabbobin mazauna garin.

A wani labarin kuma, Rundunar sojin Najeriya da yanzu haka take yakarr 'yan ta'addan Boko Haram a yankin Arewa maso gabashin Najeriya, ta yi ikirarin cewa dakarunta sun kashe kwamandojin kungiyar Boko Haram a jihar Borno.

Wata sanarwa da rundunar ta wallafa a shafinta na Twitter da safiyar ranar Lahadi ta kara da cewa dakarunta sun kwace wasu kauyuka daga hannun mayakan kungiyar.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng