Da dumin sa: Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya dawo gida daga Dubai

Da dumin sa: Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya dawo gida daga Dubai

Da dumin sa yanzu labarin da ke iske mu na nuni ne da cewa dan takarar shugaban kasa a jam'iyyar adawa ta Peoples Democratic Party (PDP), Alhaji Atiku Abubakar ya dawo gida Najeriya daga kasar Dubai.

Atiku Abubakar din dai ya tafi kasar Dubai ne tare da tawagar sa kunshe da jama'a da dama magoya bayan sa da jam'iyyar Peoples Democratic Party, inda suka shafe kwanaki suna shirya yadda za su tunkari zaben 2019.

Da dumin sa: Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya dawo gida daga Dubai
Da dumin sa: Dan takarar shugaban kasa, Atiku Abubakar ya dawo gida daga Dubai
Asali: Twitter

KU KARANTA: Musulunci ya sama karuwa a garin Jalingo

Legit.ng Hausa ta samu cewa jirgin tsohon mataimakin shugaban kasar ya diro Najeriya ne da misalin karfe 12 na daren ranar Lahadi tare da mukarraban nasa.

A wani labarin kuma, Labarin da muka samu daga majiyar mu ta Blue Print, ya na nuni ne da cewa jim kadan bayan saukar jirgin dake dauke da dan takarar shugaban kasar Najeriya na jam'iyyar Peoples Democratic Party, Atiku Abubakar, jami'an tsaro suka shiga bincikar sa.

Tsohon kakakin jam'iyyar na APC, Mista Timi Frank wanda kuma ke cikin tawagar tsohon shugaban kasar shine ya bayyanawa majiyar ta mu hakan a garin Abuja, babban birnin tarayyar Najeriya.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Asali: Legit.ng

Authors:
Mudathir Ishaq avatar

Mudathir Ishaq Mudathir Ishaq is the head of the Hausa desk at Legit.ng. He studied Industrial Chemistry as first degree at the University of Abuja, Journalism (CSR Specialization) with the Michigan State University and runs MSc Industrial Chemistry from the Nasarawa State University, Keffi. With more than a decade experience in news reporting and content editing, he has interviewed influential personalities. He can be reached on: mudathir.ishaq@corp.legit.ng