Dandalin Kannywood: Rahama Sadau ta baiwa wani da yace yana son ta an sa a dandalin sada zumunta

Dandalin Kannywood: Rahama Sadau ta baiwa wani da yace yana son ta an sa a dandalin sada zumunta

Daya daga cikin fitattun jarumai a masana'antar shirya fina-finan Hausa ta Kannywood watau Rahama Sadau ta gamu da masoyin ta a dandalin sadarwar zamani da ya roki Allah ya ba shi mata kamarta idan ba zai same ta ba.

Shi dai Khamisu S. Guyaba ya wallafa sako ne a shafin Twitter inda ya nuna matukar son da yake yi wa Rahama domin ya aure ta.

KU KARANTA: Duk wani guntun dan iska ya kuka da kan sa - Hafsan sojin Saman Najeriya

Legit.ng Hausa ta samu cewa ya kara da cewa idan hakan ba za ta yuwu ba yana so ya auri mai hali da ilimi da nutsuwa da kuma taimakon jama'a kamarta.

Masu bibiyarsa a shafin Twitter sun taya shi addu'a inda wasu ke cewa Allah ya cika masa burinsa yayin da wasu ke yi masa addu'ar zabi mafi alheri.

Daga bisani ne jarumar ta ba shi amsa inda ta roki Allah ya ba shi matar da ta fi ta sannan ta yi masa godiya.

"Allah ya ba ka wacce ta fi Rahama da komai. Na gode sosai," in ji jarumar.

Rahama Sadau ta dade tana jawo ce-ce-ku-ce a Kannywood ko da yake ta kwana biyu ba ta shiga bakin jama'a ba sakamakon karatun da ta tafi karowa a kasar Cyprus.

Muhimmiyar sanarwa: Shafin NAIJ.com Hausa ya koma legit.ng Hausa. Mun gode da kasancewarku tare da mu.

Latsa wannan domin samun labarai a wayar ku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en

Ku biyo mu a shafukanmu na dandalin sada zumunta:

Facebook: https://web.facebook.com/legitnghausa?_rdc=1&_rdr

Twitter: https://twitter.com/legitnghausa

Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari,

Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com

Source: Legit.ng

Tags:
Mailfire view pixel