Karar kwana: Tawagar wani dan takarar gwamnan APC ta murkushe mata 2 har lahira a Rivers
- Tawagar Tonye Cole, dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC ta murkushe wasu mata 2 har lahira da mota
- Rahotannin sun bayyana cewa Cole na kan hanyarsa ta zuwa Otapha, don gudanar da wani taron yakin zabe na wayar da kan gundumomi, a lokacin da hatsarin ya afku
- Jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda na jihar, Mr. Nnamdi Omoni, ya ce Cole da rundunar 'yan sandan na kan tattaunawa da iyalan mamatan da kuma wacce ta jikkata
Tashin hankali ya mamaye al'ummar garin Abua da ke cikin karamar hukumar Abua/Odua, jihar Rivers, sakamakon wani mummunan iftila'i da ya fada masu a ranar Juma'a, inda tawagar Tonye Cole, dan takarar gwamnan jihar karkashin jam'iyyar APC ta murkushe wasu mata 2 har lahira da mota.
A cewar wani rahoto, lamarin ya auku ne da yammacin rnar Juma'ar, a yankin Egbolom, kan babban titin Ogonokom, a garin Abua, inda kuma wata matar daban ta tsallake rijiya ta baya baya, amma ta samu raunuka.
Rahotannin sun bayyana cewa Cole na kan hanyarsa ta zuwa Otapha, don gudanar da wani taron yakin zabe na wayar da kan gundumomi, a lokacin da hatsarin ya afku.
KARANTA WANNAN: Makomar Oshiomhole a APC: Buhari, Osibanjo, Tinubu, gwamnoni za su gana mako mai zuwa

Asali: Depositphotos
Jami'an da ke tsaron dan takarar gwamnan, a wani kokari da suka yi na kaucewa wani mahayin keke da ke tafiya kan titin, sun karkatar da motar har zuwa karshen titin, inda kuma nan take suka murkushe mata 2 da ke tafiya a kasa har lahira.
Wani da lamarin ya faru a gaban idonsa, wanda ya bayyana sunansa da Kipoye, ya shaidawa manema labarai cewa tawagar Cole ce ta buge matan 2 a Egbolom, a lokacin matan suna tafiya a kasa, a gefen titin.
"A yanzu haka dai, an kai matan 2 da suka mutu dakin ajiye gawa. Sai dai bamu iya gane ko suwaye matan ba, ko kuma sanin inda suka fito. Amma dai daga alama mazauna garin Egbolom ne," a cewarsa.
KARANTA WANNAN: Babbar magana: INEC ta cika alkawarinta na haramtawa APC gabatar da 'yan takara a jihar Zamfara
Ko da aka tuntube shi, jami'in hulda da jama'a na rundunar yan sanda na jihar, Mr. Nnamdi Omoni, ya tabbatar da faruwar lamarin, inda ya kara da cewa Cole da rundunar 'yan sandan na kan tattaunawa da iyalan mamatan da kuma wacce ta jikkata.
Da ya ke jawabi kan faruwar lamarin, sakataren watsa labarai na APC a jihar, Mr; Chris Finebone, ya ce suna kan hanyarsu ne ta zuwa gunduma ta 8 a Abua/Odual, lokacin da hatsarin ya afku, inda ya bayyana cewa an soke dukkanin wasu harkokin siyasa na wannan ranar.
SANARWA: Shafin jaridar NAIJ.com Hausa ya sauya suna zuwa Legit.ng Hausa. Muna fatan za ka ci gaba da kasancewa tare da Legit.ng Hausa don karanta labarai da dumi duminsu.
Latsa wannan domin samun sabuwar manhajar labarai ta Legit.ng Hausa a wayarku ta hannu: https://play.google.com/store/apps/details?id=com.naij.hausa&hl=en
Ku biyo mu a shafukan mu na dandalin sada zumunta:
Facebook: https://facebook.com/legitnghausa
Twitter: https://twitter.com/legitnghausa
Idan kuna da wata shawara ko bukatar bamu labari, Tuntube mu a: labaranhausa@corp.legit.com
Asali: Legit.ng